Trump ya sallami mai ba shi shawara Anthony Scaramucci

Scaramucci Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori daraktan sadarwa na fadar White House Anthony Scaramucci kusan kwana goma bayan an nada shi kan mukamin.

Mr Scaramucci ya sha suka bayan ya bukaci wani dan jarida ya caccaki abokan aikinsa.

Shugaban ma'aikatan Shugaba Trump Reince Priebus da kakakinsa Sean Spicer sun bar aikinsu ne bayan an nada Scaramucci.

Sabon shugaban ma'ikatan Mr Trump John Kelly ne ya dauki matakin korar Scaramucci bayan an rantsar da shi ranar Litinin.

Wata sanarwa mai layi uku da aka fitar daga fadar White House ta ce: "Anthony Scaramucci zai sauka daga mukaminsa na daraktan sadarwa na White House.

"Mr Scaramucci yana ganin zai fi kyau ya bai wa shugaban ma'aikata John Kelly damar kafa tawagarsa. Muna yi masa fatan alheri."

Tsohon daraktan sadarwar ya sha yin takama cewa yana bin umarnin shugaban kasa ne ba na shugaban ma'aikatansa ba.

Labarai masu alaka