'Idan na sha shayin sai in kwana ina tuki ban gaji ba'

Motoci da babura a titinan Nijeriya Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Masu motocin dai na zargin masu baburan a daidaita-sahun da yawan haddasa hadari da kuma karce musu jikin motocinsu

Ana zaman doya da man-ja tsakanin masu motoci da matuka babur mai kafa uku da aka fi sani da a-daidaita-sahu a birnin Kano da ke arewacin Nigeria.

Masu motocin dai na zargin masu a-daidaita-sahun da yawan haddasa hadari, da kuma karce ko musu jikin motoci da gangan.

Sai dai shugabannin masu baburan sun musanta zargin, suna cewa cikakkun mambobin kungiyarsu ba sa taka doka.

Afkuwar hadura masu nasaba da matuka baburan na a-daidaita-sahu na neman zama ruwan-dare a kan manyan titunan da ke birnin Kano.

Alhaji Alhasan Sa`idu wani mai mota ne da ya shaida wa BBC cewa ya daina yi wa motarsa fenti irin na kwalisa saboda ya gaji da asara:

'' Masu baburan a daidaita-sahu sun dauki masu motoci kamar kishiyoyinsu,'' motoci daya-daya ne za ka ga masu wadannan babura ba su karce ba''.

Amma wasu masu baburan kamar Malam Nafi'u Hussaini na zargin cewa masu mota ne da laifi, yana mai cewa ko kadan masu motoci ne ba sa saurara musu;

'' Rashin hakuri ne ya ke kawo haka, ake ganin kamar ganganci ne muke yi, lokuta da dama za ka ga masu mota ba sa son su daga mana kafa.''

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Hukumar Karota ta ce tana iya bakin kokarinta wajen sa ido kan tukin ganganci a fadin birnin

Sai dai mafi yawan jama`ar gari sun fi zargin masu a daidaita sahu da tukin gaggawa da kuma ganganci, sakamakon zargin da ake yi cewa wasunsu na shan kayan kara kuzari da kan fi karfinsu.

Akwai teburan masu sayar da shayi a sassan birnin Kanon daban-daban da aka fi sani da gadagi wanda masaya sukan yi masa cincirindo, ciki har da matuka a daidaita sahun.

Daya daga cikin matuka baburan ya shaida wa BBC cewa yana amfani da shayin ne don ya saboda amfani a jiki, ya kuma kara da cewa;

'' Ina shan bakin shayi, saboda yana maganin rana, wanda idan na sha sai in kwana ina tuki ban gaji ba''.

Sai dai masu sayar da shayin da dama na cewa ba sa saka kwayoyi ko kayan kara kuzari a shayin nasu.

Alhaji Sani Sa`idu Dankoli shi ne shugaban kungiyar matuka babura masu kafa uku na jihar Kano, wanda ya ce suna sane da korafe korafen da ake yi a kan `ya`yan kungiyar:

'' Akwai tsarin da muka fito da shi, gwamnati ta hada mu da hukumar VIO, muna kai wadannan 'ya'yan kungiya tamu ana wayar musu da kai''.

Kakakin hukumar Karota mai sa-ido a kan masu ababan hawa a jihar Kano, Mallam Murtala Salisu ya shaida wa BBC cewa suna matukar kokarin daukar matakai kan masu baburan da matuka mota.

'' Muna sane da wannan matsala, kuma muna kokarin mu ga cewa wannan matsala ta kau, ta hanyar hada taron bita ga matuka baburan haya din.''

Zuwan a daidaita sahu dai ya taimaka gaya wajen saukaka sufuri a birnin Kano, ya kuma rage munanan raunukan da akan ji da Babura masu kafa biyu, inda wani lokaci ake karairayewa, ko ma asarar rayuka.

Labarai masu alaka