Ba ma goyon bayan rushe tsarin jihohi 36- Edwin Clark

Edwin Clark shugaban kungiyar dattawan yankin Niger Delta a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Yankin na Niger Delta dai ya sha korafin cewa an mayar da shi tamkar inuwar giginya, inda aka fi maida hankali wajen gina wasu sassan kasar

A Nigeria, har yanzu al'ummar kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da kiraye kirayen da wasu ke yi na neman sake fasalin kasar.

A wata hira da BBC, shugaban kungiyar dattawan yankin Niger Delta Chief Edwin Clark ya ce, ba sa goyon baya a rushe tsarin jihohin 36 da ake da su domin komawa tsarin shiyyoyi shida kamar yadda wasu ke kiraye-kiraye.

Ya ce kamata ya yi a koma abinda magabatan kasar irin su sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, da Dr Nnamdi Azikwe, da kuma Cif Obamfemi Owolowo suka amince da shi a shekarar 1953 cewa su kafa tsarin kasa guda ta yadda ko wace shiyya cikin shiyyoyi uku za ta samu kwarya-kwaryar cin gashin kanta.

''Idan aka yi haka za samu daidaito a kasar, kuma ko wace shiyya za ta samu bunkasa daidai karfinta.''

Mr Clark ya kuma ce ba maganar sanya wata jiha ta fi wata jiha arziki ba ne, kowace jiha za ta iya aiki na kashin kanta idan tana da arzikin gona ta bunkasa shi ta sayar da amfanin da ta samu, idan tana da albarkatun kasa ita ma ta yi haka, amma za ta rika bayar da wani kaso ga gwamnatin tarayya a matsayin haraji.

Yankin na Niger Delta dai ya sha korafin cewa an mayar da shi tamkar inuwar giginya, inda aka fi mai da hankali wajen gina wasu sassan kasar mussamman arewaci wanda baya samar da mai.

Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, wani dan siyasa kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano arewacin Nijeriyar; shi ma ya ce kamata ya yi a jarraba tsarin bai wa kowace shiyya wani kaso na musamman ta fitar da ajandar ta.

'' Wannan mai da gas da ake nema a arewa a ma ida hankali a ga an samu su, na biyu kuma wutar lantarki, idan suka ga duk wadannan abubuwa an same su to za a zauna lafiya.''

Alhaji Gwarzo ya kuma ce sai a fito a duba k wace jiha a ga me Allah ya ba ta, in aka yi haka sai a tsaya a dau tsawon kamar shekara biyar a ga cewa an fito da wadannan abubuwa don ita wannan jiha ta zauna da kafafunta.

'' Idan aka yi haka su sauran jihohin kudu da suke ganin mu cima-zaune ne za su ga cewa ashe muna da amfani''

Labarai masu alaka