Boko Haram: Shugabannin sojin Nigeria sun koma Maiduguri

Olonisakin Hakkin mallakar hoto Nigeria Defence
Image caption Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ne ya jagoranci sauran hafsoshin sojin zuwa Maiduguri

Manyan hafsoshin sojin Najeriya sun isa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar domin tunkarar wani gagarumin shiri na yakar kungiyar Boko Haram.

A makon da ya gabata ne Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarce su da su koma can bayan wani mummunan hari da kungiyar ta kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 40.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya Janar Usman Kuka-Sheka ya shaida wa BBC cewa da sanyin safiyar ranar Talata ne hafsoshin son suka isa birnin, wanda shi ne cibiyar masu tayar da kayar bayan.

Ya ce babban Hafsan Hafsoshin kasar Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ne ya jagoranci sauran hafsoshin sojin da suka hada da shugaban sojin kasa Laftanal Janar Tukur Buratai da na sama Air Marshal Sadique Abubakar.

Janar Kuka-Sheka ya ce babban hafsan rundunar sojin ruwa na kasar ne kawai ba ya cikin tawagar saboda ya yi tafiya, amma shi ma wakilansa na can.

Harin da Boko Haram ta kai wa tawagar masu binciken mai na NNPC, wanda shi ne mafi muni a bana da ta kai, ya tayar da hankalin al'ummar kasar.

Ya kuma janyo suka ga jami'an tsaron kasar, ganin yadda da farko suka ce sun kubutar da mutanen amma daga bisani sai Boko Haram ta fitar da hoton bidiyon wasu daga cikin mutanen.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A baya ma an taba bai wa shugabannin sojin irin wannan umarni amma wasu na ganin bai yi tasiri ba

Sannan kuma rahotanni suka tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu ya karu matuka.

Tuni dai shugabannin sojojin suka isa babbar cibiyar gudanar da ayuukan soji da ke Maidugurin.

Ministan tsaron Najeriya ya ce za a sayi karin kayan aiki na zamani wadanda za su bai wa jami'an tsaro damar ganin abokan gaba daga nesa.

Mafi yawancin mutanen da aka kashe a harin na makon jiya a jihar Borno sojoji ne da 'yan sintiri ko kuma 'yan kato da gora.

Labarai masu alaka