Nigeria: 'An kama masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna'

Kidnappers Hakkin mallakar hoto Nigeria Police Force
Image caption Wannan ba shi ne karo na farko da rundunar 'yan sandan Najeriya za ta ce ta kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna ba

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu masu garkuwa da mutane da suka addabi jama'a a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin rundunar 'yan Sandan Najeriyar, Jimoh Moshood, ya gabatar da mutum 32 da ake zargi da garkuwa da mutane a garin Katari da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rundunar 'yan sandan ta ce an kama wadanda ake zargi da garkuwa da mutanen ne bayan Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Idris Kpotun, ya tura jami'an 'yan sanda na musamman kan hanyar domin dakile ayyukan masu garkuwa da mutane.

Bayan haka ne Sufeto Janar na 'yan sandan kasar ya bayar da umurnin a sauya wa dukkan jami'an 'yan sandan da ke aiki a kan hanyar wurin aiki.

A cikin jami'ai na musamman da suka taimaka wurin kama mutanen, akwai fitaccen dan sandan nan, ACP Abba Kyari.

Garkuwa da mutane dai a kan hanyar, wadda ke cikin wadanda aka fi amfani da ita a arewacin Najeriya, wata matsala ce da ta ki ci ta ki cinyewa, duk da cewa rundunar 'yan sandan kasar ta ce ta kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a kan hanyar a kwanakin baya.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption An kama makamai a hannun mutanen
Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya sa matafiya na fargabar bin hanyar

Labarai masu alaka