Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 200 a India

Hoton jihar Gujurat kenan, da sojin saman kasar India suka dauka a ranar 25 ga watan Yuli da ya wuce, hoton ya nuna yadda ruwa ya daidaita kauyukan da ke jihar, sakamakon ambaliyar ruwan. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Adadin wadanda suka rasu sun rubanya, kwanaki biyu da yin ambaliyar ruwan

Mummunar ambaliyar ruwan da ta afkawa wasu yankunan jihar Gujarat a kasar Indiya ta hallaka sama da mutum 218, kamar yadda jimi'an gwamnati suka tabbatar.

Kwanaki biyu da yin ambaliyar ruwan, aka sake gano wasu karin gawawwakin sama da mutum 100.

Jami'an jihar sun tabbatar da cewa, ambaliyar ruwan ta shafi a kalla mutum 450,000.

A bana kadai jihohi 20 ne suka fuskanci ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar Indiya.

Haka kuma a arewa maso gabashin jihar Assam ma an fuskanci ambaliyar inda mutane da dama suka mutu, wasu daruruwa suka rasa muhallansu.

Gwamnatin Indiya ta sanar da cewa za ta aike da kayan agaji ga wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma tuni Firai minista Narendra Modi ya sanar da kai ziyara jihar Assam a ranar Talata, domin jajantawa al'ummar yankin.

Ya kara da cewa makasudin kai ziyarar shi ne samar da maslaha ta dindindin da jihar Assam ke fuskanta a ko wacce shekara.

Kamfnanin dillancin labaran Indiya ya ambato wani jami'in gwamnati na cewa yawancin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar Gujarat sun fara komawa kauyukansu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kididdigar gwamnati ta tabbatar da mutane 450,000 ne ambaliyar ruwan jihar Gujarat ta shafa
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mamakon ruwan saman da aka sheka ya janyo lalacewar hanyoyin sufuri ciki har da titin jirgin kasa

Labarai masu alaka