‘Saudiyya tana gina wajen shakatawa a Bahar maliya’

Wannan hoton tekun bahar maliya na Saudiyya. Hakkin mallakar hoto Kingdom of Saudi Arabia
Image caption Kwararru sun bayyana za ayi amfani da wurin mai girman mil 125, da yake tekun bahar maliya.

Saudiyya ta sanar da gagarumin aikin da za ta yi, ta amfani da tsuburai 50 don gina wurin shakatawa mafi girma a kasar, da za a gina a cikin tekun bahar maliya.

Saudiyya dai ta dauki wannan mataki ne domin jan hankalin masu yawon bude ido daga sassa daban-daban na duniya, a kokarin da kasar ke yi na rage dogaro ga man fetur da darajarsa ta karye a kasuwannin duniya.

Hukumomi sun ce za a rage tsauraran matakan da mutane ke fuskanta kafin samun bisar shiga kasar, inda wannan bangare na masu yawon bude ido da shakatawa, za su samu cikin sauki.

Sai dai kawo yanzu ba a bayyana yanayin shigar da musu yawon bude idon za su yi ba a kasar da ta zamo tushen addinin musulunci a duniya baki daya.

Dama dai shan giya, da gidajen silima da na rawa haramtattu ne a kasar Saudiyya.

Haka kuma dole mata a kasar su suturce jikinsu, ta hanyar sanya suturar da ba matsattsiya ba, tare da rufe gashin kansu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A dokar kasar Saudiyya ba a amince mata su tuka mota ba, ko yin tafiya su kadai ba tare da muharramansu ba.

A shekarar 2019 ne za a fara gabatar da aikin, inda za a fara da gina katafaren filin jirgin sama, da manyan otal-otal na alfarma, da gidaje ga masu sha'awar kamawa, kuma a shekarar 2022 ake sa ran kammala wannan aikin.

Wakilin BBC kan al'amuran kasashen labarawa ya rawaito cewa ba bakon abu ba ne ga kasar Saudiyya, idan aka yi batun shiga da fitar baki, inda a duk shekara miliyoyin musulmai na tururuwa zuwa kasar mai tsarki don gudanar da ibada a lokutan aikin Hajji da Umarar watan azumin Ramadan da ke faruwa a duk shekara.

Sannan a sauran watanni 10 na shekarar kafa ba ta daukewa ga masu ibadar, haka nan miliyoyin ma'aikata su ma na turuwa don gudanar da ayyuka.

Sai dai batun bin dokoki da ka'idojin da addinin musulunci ya shimfida a kasar, daga kan sanya sutura da rashin gudanar da harkokin shakatawa na daga cikin dalilan da masu yawon bude ido ke dari-dari da ziyartar kasar.

Wannan dai wani bangare ne na kokarin da yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ya ke yi, wanda aka yi wa lakabi da 'Muradun shekarar 2020' ko 'Vition 2020' a turance. A kokarin karkatar da akalar yin ayyukan da kasar za ta samu kudaden shiga da nufin rage dogaro da man fetur da yawancin kasashen duniya suke yi, a daidai lokacin darajar danyan mai ta ragu a kasuwannin duniya.

Haka nan bude wurin na nufin samar da karin ayyukan yi ga 'yan kasar, Sannan zai zamo aiki na farko mafi girma da aka yi a kasar da ya danganci masu yawon bude ido.

Cikin abubuwan da za a yi da za su janyo hankalin masu yawon bude ido sun hada da, dutsen da zai din ga zubo da ruwa, da wasu namun daji da ba safai ake samun su ba sai a kasashen labarawa, misali tsuntsun nan mai kama da shaho da sarakuna da attajiran larabawa ke amfani da su wajen farauta ko shakawatawa idan aka fita kilisa.

Masu yawon bude idon za su samu damar kai ziyara rusasshiyar daular Madain Saleh, wurin da hukumar kula da kayan tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana daya daga cikin wuraren tarihi na duniya.

Hakkin mallakar hoto Kingdom of Saudi Arabia Ministry of Information
Image caption Tsohuwar daular Madain Saleh a kasar Saudiyya

Labarai masu alaka