Gwamnati za ta gyara wurin tarihin da Boko Haram ta lalata

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Yusuf Abdallah kan Wurin Tarihin Sukur

Kuna iya latsa alamar lasifika da ke jikin hoton sama, dan sauraran hirar da Habiba Adamu ta yi da shugaban hukumar da ke kula da wuraren adana kayan tarihi a Najeriya, Yusuf Abdallah.

Wurin ajiyar kayan tarihi na Sukur a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya wuri ne mai dadadden tarihi.

Shi ne na farko da hukumar bunkasa ilmi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta sanya a matsayin wajen tarihi na farko a nahiyar Afrika a shekarar 1999.

Yayin da wurin tarihi na Osun-Osogbo ya kasance wuri na biyu da Majalisar ta sanya a matsayin wajen tarihi a Najeriya.

Ya kuma shafe dubban shekaru ba tare da wani sauyi ba.

Hukumar da ke sa ido a kan wuraren adana kayan tarihi ta Najeriyar ta ce tana shirin gyara cibiyar tafinta da wasu abubuwan da mayakan Boko Haram suka lalata a wajen.

Shugaban hukumar Malam Yusuf Usman ya shaida wa BBC muhimmancin wurin tarihi na Sukur da cewa baya ga kasancewa wurin adana kayan tarihi na farko a nahiyar Afirka da UNESCO din ta ba shi wannan matsayi, shine na farko a Nijeriya.

''Yana da muhimmanci kwarai wajen taimaka wa gwamnati ta bunkasa harkar yawo bude ido'',wurin yana kan dutse, kuma mutanen garin sun yi amfani da duwatsu da suka rika jera wa suka yi gine-gine daban-daban''.

Hakkin mallakar hoto Google

Gine-ginen dai sun hada da gidajen sarakunansu, da wuraren bautarsu, da kuma gidajen abubuwan da suke amfani da su, in ji Malam Usman.

Ya kuma kara da cewa; ''Irin hikimar da mutanen wurin ke da shi da kuma yadda suke sarrafa abinda suke da shi su kuma yi abubuwan da za su taimake su shine babban dalilin da ya sa aka karrama wurin.''

Wasu rahotanni dai sun ce mayakan Boko Haram sun lalata wurin a lokacin da suka kai farmaki a yankin.

Sai dai kuma shugaban hukumar kula da wuraren kayan tarihin Malam Usman din ya ce mayakan ba su lalata ainihin wurin ba.

''A shekara ta 2014 mayakan suka kai farmaki a wurin amma ba su lalata wurare masu muhimmanci a wurin ba''.

Ya ce sai dai akwai 'yan abubuwa da suka lalata da ba za a ce sun taba mutuncin wurin ba, kamar su makarantu da wurin da ake tafintar wurin tarihi sune suke son gyarawa.

Hakkin mallakar hoto National Museum
Hakkin mallakar hoto National Mesuem
Hakkin mallakar hoto National Mesuem
Hakkin mallakar hoto UNESCO
Image caption Mutanen garin sun yi amfani da duwatsu da uka rika jera wa suka yi gine-gine daban-daban

Labarai masu alaka