Barayi 'sun wawashe' gidan Goodluck Jonathan na Abuja

Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jonathan ya yi mulkin Najeriya tsawon shekara shida

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce barayi sun shiga gidansa da ke unguwar Gwarinpa a babban birnin kasar Abuja, inda suka yi masa sata ta hanyar dauke duk wani abu da za su iya a gidan.

A wata sanarwa da mai magana da yuwunsa Ikechukwu Eze ya fitar, ya ce a watan da ya gabata ne aka gano satar da aka yi din, sakamakon sanar wa hukumomin 'yan sanda da aka yi.

"Barayi sun shiga gidan, wanda tsohon shugaban kasar ya saya a wajen kamfanin CITEC da ke gina gidaje a shekarar 2004, suka sace duk wasu kaya da hannu zai iya kawar da su kamar gadaje da kujeru da kayan lantarki da kayayyakin bandaki har da kofofi da tagogi," in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, nan da nan 'yan sanda suka shiga bincike wanda hakan ya yi sanadin kama wasu daga cikin wadanda ake zargi.

Shida daga cikin wadanda aka kama din 'yan sandan da suke gadin gidan ne a cewar sanarwar.

Sai dai hukumar 'yan sanda ta fitar da tata sanarwar inda ta ce ta kama 'yan sandan da ke gadin gidan ne don tambayarsu yadda abin ya faru, amma ba ta fadi yawan 'yan sandan da ta kama ba, kamar yadda bangaren Mista Jonathan ya fada.

Hakkin mallakar hoto Premium Times
Image caption Jonathan ya sayi gidan ne a shekarar 2004 daga kamfanin CITEC

Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Sai dai Mista Eze ya ce, wasu kafofin yada labaran sun zuzuta yawan kayan da aka sace din, inda suke cewa an sace talbijin 36 da firinji 25.

"Abubuwan da aka sace sun hada da talbijin shida da firinji uku da kuma na'urar dafa abinci guda daya," acewar sanarwar.

A karshe Mista Eze ya mika godiyarsu ga dukkan 'yan Najeriya kan yadda suka nuna damuwarsu da kuma sakon jajen da suka dinga aikewa Mr Jonathan.

Labarai masu alaka