'Maza za su dinga auren matan da suka yi wa fyade a Jordan'

Wasu mata da suka fito zanga-zanga a birnin Amman na kasar Jordan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jordan na daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya ma su doka irin wannan

'Yan majalisar kasar Jordan sun kada kuri'ar da za ta ba su damar yi wa dokar fyade garanbawul da za ta sanya maza su auri matan da suka yi wa fyade.

Majalisar wakilai ta amince a cire tsohon hukuncin da ake zartarwa a kan mazan, mai cike da cece-kuce wanda aka fi sa ni da Article 308.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun dade suna fafutuka da kiraye-kirayen a dauki matakin, wanda zai kare matan da abin ya shafa daga tsangwama da samun ingantacciyar rayuwa.

To sai dai kuma, dole sai majalisar dokoki ta rattaba hannu akai kana Sarkin Jordan ya amince da ita kafin ta zama doka.

Kasar Jordan na daya daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, da suke da doka irin hakan har a kundin tsarin mulkin kasar.

A makon da ya gabata ma kasar Tunisiya ta dauki mataki shigen irin na Jordan, yayin da ake sa ran kasar Labanon za ta bi bayan takwarorinta don sauya hukuncin fyade a kasar.

'Nasara'

Masu fafutuka sun yi maraba da wannan sabuwar doka, a kasar da ke kwaikwayon kasashen yammacin duniya a wasu harkokin rayuwarsu.

Wata mai fafutuka kuma ma'aikaciya a ofishi mai kula da harkokin mata a Jordan, Salma Nims ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, wannan kuri'a da 'yan majalisar suka kada babbar nasara ce ga matan kasar da wadanda suka dade suna fafutuka don tabbatar da hakan.

Dokar baya dai ta tanadi cewa duk wanda ya yi wa mace fyade kuma yake son a sauya masa hukunci, dole ya aureta, kuma za a iya yafe masa hukuncin matukar suka zauna har tsahon shekara uku ba tare da ya sake ta ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasar Jordan na daya daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, da suke da doka irin hakan har a kundin tsarin mulkin kasar

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun so ci gaba da amfani da tsattsauran hukunci, ga wadanda ake zargi da yin jima'i da kananan yara 'yan shekara 15 da 17, wadanda kuma ba tilasta musu yi ko fyade akai musu ba, sun yi ne bisa radin kansu.

Kungiyar kare hakkin bil'adam ta Human Rights Watch, ta ce kasashen gabas ta tsakiya da yammacin Afirka da har yanzu suke amfani da dokar sun hada da kasashen Algeriya, da Iraki, da Kuwait, da Syria, da wasu kasashen da ke yankin Palasdinawa.

Labarai masu alaka

Karin bayani