Ana yi wa 'yan Shi'a kora da hali a Saudiyya — MDD

Map of Saudi Arabia

Rahotanni sun ce daruruwan mutane ne suka tsere daga garin Awamiya da ke gabashin Saudiya, sakamakon makwannin da aka kwashe ana fafatawa tsakanin masu tayar da kayar baya da jami'an tsaro.

Tun a watan Mayun da ya wuce hukumomin kasar ke kokarin rusa tsohon garin Awamiya, inda rahotanni ke cewa masu tayar da kayar baya kuma mabiya darikar Shi'a na amfani da garin a matsayin maboya.

Sai dai masu fafutuka sun zargi jami'an tsaro, da tilastawa mazauna garin barin muhallansu.

Wannan ita ce fafatawa mafi girma da aka taba yi a yankin da mabiya darikar Shi'a ke da rinjaye a kasar Saudiyya.

A kalla mutum bakwai ne suka rasu, ciki kuwa har da 'yan sanda biyu a hatsaniyar da aka yi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

Masu fafutuka a yankin sun ce dakarun kasar, sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi kan gidaje da motocin jama'a, kuma harsashi ya lalata yawancin gine-ginen yankin.

Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin Saudiyya, su taimake su don barin yankin, yayin da kafafen yada labaran kasar ke cewa an bai wa mutanen gidaje a garuruwa makofta.

Mabiya darikar Shia, da ke zaune a kusa da birnin Qatif, sun dade da yin korafin an mayar da su saniyar ware, yayin da masarautar kasar ta yi halin ko in kula kan musguna musu da ake yi.

Ko a watan Mayu sai da Majalisar Dinkin Duniya ta soki matakin da gwamnati ta dauka na rushe wata tsohuwar unguwa mai suna al-Masora mai cike da tarihin shekara 400 a garin Awamiya, inda kusan mutane 3,000 ke zaune, wanda hakan barazana ce ga kayan tarihi na duniya.

Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan harkokin gidaje a kasar, Lailani Farha, ta bayar a rahoton cewa tun da fari hukumomin Saudiya sun yi wa mazauna garin kora da hali ta hanyar yanke musu wutar lantarki.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Wani rubutu da aka yi kan kisan fitaccen malamin mabiya darikar Shi'a Nimr al-Nimr da gwamnati ta yi a garin Awamiya

A shekarar 2011 ne guguwar juyin juya hali ta fara kadawa a yankin gabas ta tsakiya, daga nan zanga-zanga da boren kin jinin matakai da salon mulkin shugabannin kasashen Larabawa da yawan kai hare-hare suka kara yaduwa.

Haka kuma tun bayan kisan malamin Shi'a Sheikh Nimr al-Nimr da hukumomin Saudiya suka yi a watan Janairun shekarar 2016 ya kara samawa rashin zaman lafiya wurin zama a kasar.

Shaihin malamin, wanda ya yi fice kan adawa da gwamnatin Saudiyya na zaune ne a garin na Awamiya.

A watan Yuli ma hukumomin kasar sun yanke tare da zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane hudu da gwamnatin ta ce ta same su da hannu a harin ta'addanci da aka kai yankin Qatif.

Duk dai a wannan watan, wasu hare-hare mabanbanta da aka kai garin Awamiya ya hallaka jami'an tsaro biyu. Yayin da a watan Yuni ma wani jami'in tsaron ya rasu a wani harin da aka kai garin.

An gudanar da gagarumar zanga-zanga, a kuma lokacin masu fafutuka suka zargi jami'an tsaro da budewa masu boren wuta, tare da kama wasu daga cikinsu da har yanzu ake tsare da su a gidajen kason kasar wasu kuma tuni aka zartar da hukuncin kisa a gare su bi sa zargin shiga zanga-zangar da gwamnati ba ta amince da ita ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani