Barayi sun sace tirela makare da wayar iPhone 7

Hotunan kwalayen wayar salular samfurin iPhone 7 wadda aka dauki hoton a ranar 16 ga watan Satumbar, 2016 a birnin London Hakkin mallakar hoto JACK TAYLOR/AFP/Getty Images
Image caption Barayin sun yi amfani da wata motar ta daban, inda suke jefa manyan kwalayen da wayoyin suke, wadda ke tafiya kan babbar hanya

A kasar Neitherlands aka cafke mutanen biyar da suka fito daga kasar Romania, wadanda ake zargi da sace wayoyin iPhone 7, da suka kai $590,000, a lokacin da babbar motar daukar kayan ke tafiya a babbar hanya.

An yi zargin sun yi ta bin motar sau da kafa, daga bisani daya daga cikinsu ya yi tsalle ya dane motar, ya fasa wani gilashi ya shiga cikin ta.

Daga nan sai ya fara miko manyan kwalayen da wayoyin ke ciki ta saman motar, sauran abokan satar shi na karba suna zubawa a cikin tasu motar samfurin bas ta diban kaya.

Lamarin ya faru ne a daren 24 ga watan Yuli, a kan wani babban titin.

Kamfanin dillancin labaran kasar ED, ya rawaito cewa irin wadannan gungun barayin kan yi wa motarsu kwaskwarima da kawata ta, amma cikin motar fayau yake anan suke jibga kayan da suka sata.

Irin wannan satar kasadar, a kasar Jamus aka fara ganin ta a shekarar 2008.

Haka kuma an ga sata makamanciyar hakan a kasar Belgium, kuma dukkan sace-sacen wayoyin zamani na komai da ruwan ka ake sacewa.

Masu satar na amfani da karfe ko abin buga iska wajen fasa tagar ko bayan mota.

Mai magana da yawun 'yan sandan kasar Ed Kraszewski, ya ce ana gudanar da bincike kan yawaitar sace-sacen da ake yi wa manyan motocin daukar kaya, sai dai ya dasa ayar tambaya kan ko za a iya magance satar irin wannan cikin sauki.

Ya kara da cewa, "motocin da aka yi wa sata irin wannan ko tsayawa ba su yi ba a lokacin da ake satar, don haka wayoyin salular sun bata kenan. Sai daga baya ne muka samu shaidu da motar da aka yi satar da ita."

Wadanda ake zargi da satar sun kai shekara 33, da 'yan 43, an kuma kama su ne a ranar Asabar a wani wurin shakatawa da iyalai ke zuwa a karshen mako da ke yankin Otterlo, a gundumar Gelderland.

'Yan sandan sun gano wayoyin iPhone din da adireshin wurin, anan ne kuma suka ga motar da ake zaton da ita aka yi satar.

A ranar Talata mai zuwa ake sa ran za a gurfanar da mutanen biyar a gaban kuliya.

Labarai masu alaka