Ko ya dace a koyawa 'yan makaranta yadda ake shayarwa?

Jariri na shan nono Hakkin mallakar hoto Getty Images

Likitoci sun ce Birtaniya ce kasar da ta fi kowacce kasa a nahiyar Turai karanci iyaye da ke shayar da 'ya'yansu.

Har ila yau, likitocin sun ce ya kamata a rika koyar da dalibai darrusa kan shayarwa a makaranta.

Jami'ar Royal College of Paediatrics and Child Health ta ce Birtaniya na daya daga cikin kasashen da suka fi karancin raya al'adar shayarwa a Turai, inda kashi uku ne kacal cikin jariran kasar ke shan mama har tsawon wata shida.

Wasu sun danganta hakan da yawan tsangwamarsu da ake yi.

Jami'ar ta bayar da shawarar makarantu su rika koyar da yadda shayarwa a darussan da suka hada da na kiwon lafiya da zamantakewa.

Hakazalika ta bayar da shawarar cewa ya kamata a rika bai wa iyaye mata kwarin gwiwa wajen shayar da jariransu har wata shida, inda daga bisani ake iya hadawa da abinci mai dan kauri.

'Kyankyami'

Shugabar jami'ar Farfesa Neena Modi ta ce jarirai kalilan ne ake shayarwa, kuma alhaki ya rataya a kan gwamnati da iyaye da makarantu su nema wa kasar mafita.

A cewarta, yara na bukatar fahimtar ilimin shayarwa.

"Tun da farko, ya kamata a fadakar da yara tun suna kanana, ta yadda za su rika ganin iyaye mata na shayarwa, saboda ya zame masu jiki," in ji ta.

Ta ci gaba da cewa: "sai a fara koyarwa a makarantu, inda yara ke iya ganin misalai da zai nuna yadda yake da amfani ga lafiya da kuma dalilan da ke sa ya zo da wahala ko sauki."

"Dukkan dalibai maza da mata ne ya kamata a koyar da wannan darasi, ganin yadda hadin kan ma'aurata ke da amfani matuka a lamarin," kamar yadda ta ce..

A yanzu, ilimin kiwon lafiya da zamantakewa baya cikin tsarin darussan da ake koyarwa a makarantu, amma ana shirin nazari a kai a bazarar bana.

Makarantun da ke koyar da darussan kuma, na yanke shawara ne bisa ga ra'ayinsu.

Farfesa Modi ta ce, "lokacin da muka tambayi wasu yara da kungiyoyin matasa game da tunaninsu a kan shayarwa, mun yi mamaki matuka, kuma gaskiya ran mu ya baci, saboda yadda suke amfani da kalamai na kyankyami."

Ta kara da cewa, "A gaskia ya kamata mu sauya tunanin al'umma, da kuma 'ya'yanmu."

"Wani abu mara dadi shi ne yadda mutane ke kyamar shayarwa hakan kuma ke sanya rashin kwarin gwiwar aiwatar da shi, babu masu taimakawa, babu mashawarta kuma a wuraren aiki ma babu kwarin gwiwar ga mace ta ci gaba da shayar da jaririnta," in ji farfesar.

"Bugu da kari kuma sai ka ga ana tsangwamar masu shayarwa a bainar jama'a, saboda haka ma babu mamaki yadda wasu iyaye mata ke mitar cewa suna fuskantar matsaloli."

Anna Whitehouse, wata mai sharhi kan harkokin yau da kullum a shafin Intanet mai suna Mother Pukka, ta ce ita ba ta da matsalar shayarwa cikin jama'a, amma ta san akwai wadanda ba su iya hakan.

"Ba laifinsu ba ne," in ji Anna Whitehouse, "Ba a fadakar da mutane cewa ba wani sabon abu ba ne, babu darussan kan shayarwa a ilimin halittu wato Biology, sai kwatsam ka ga ka shiga yi, kowa kuma na yi maka kallon abu ne da ya zamo maka dole."

Hakkin mallakar hoto AlIYA SHAGIVA
Image caption Hoton diyar shugaban Kyrgystan da aka dauka tana shayar da jaririnta ya janyo ce-ce-ku-ce kan shayarwa

Ra'ayoyin jama'a

Natalie Penrose ta shaida wa BBC cewa, "Wani mataki ne mai kyau, idan za a soma koyar da ilimin shayarwa a makarantu."

Ta kara da cewa, "Ni har yanzu ina shayar da diyata mai shekara daya da rabi, kuma zan so in ga hakan ya zamo abin da kowa ke yi ba wai abin da za a rika kyamata ba, domin ban san mene ne dalilin da ke sa wasu iyaye mata ba sa ci gaba da shayarwa ba."

Amma, Helen Homes, wacce malama ce kuma uwa, ta ce babu wani amfani a rika matsawa iyaye mata da cewa sai sun shayar.

Ta ce, "Ya kamata kwararru su fahimci cewa akwai mata kalilan da suka zabi shayar da jariransu madarar gwangwani, kuma yawancin sun yanke wannan shawarar ne saboda ba su samu masu agaza musu ba."

Fiona ta ce ba ta da isasshen ruwan nono lokacin da ta haifi diyarta.

"Na yi kokarin shayarwa, sosai ma kuwa, amma takura da matsin lamba da na fuskanta wajen kwararru a asibiti ya sa na ki neman taimakon kowa."

Lorna Pedersen ta ce ana yawan cewa mata suna nuna son kai da lalaci da jahilci, idan har ba su amince su shayar ba.

Gajia da Galabaita

A wani bincike da aka gudanar kan iyaye mata 1,030 da suke da yara da ke da shekaru kasa da biyar, mafi yawancin dalilan da suka bayar na daina shayarwa sun hada da;

Jaririn baya kama nonon sosai (kashi 50 cikin 100)

Rashin isasshen ruwan nono (kashi 42 cikin 100)

Zafi (kashi 39 cikin 100)

Gajiya da galabaituwa, (kashi 34 cikin 100)

Matsala wajen matso ruwan nono (kashi 32 cikin 100)

Damuwar cewa jaririn baya kiba yadda ya kamata (kashi 24 cikin 100)

Kusan kashi uku cikin hudu daga cikinsu baki daya, sun amince da cewa ana fitinar mata da zancen shayarwa, amma babu mai taimaka masu da komai.

An gano cewa wadanda ke shayarwa har tsawon mako shida, da suka samu taimako akai-akai daga kwararru kan shayarwa, sun fi samun nasara.

Justine Roberts, wacce ta kirkiro kungiyar Mumsnet, ta gudanar da wani bincike, inda ta ce, "Bai kamata ayi ta azalzala iyaye mata ba kan shayarwa, amma kuma a rika barinsu da jariransu a hannu lokacin da suke bukatar taimako."

Ta kara da cewa, "Shayarwa iyawa ce, don haka iyaye na bukatar a agaza musu, musamman yadda yawanci suke cikin wani yanayi na gajiya da rashin bacci."

Wasu shawarwari da jami'ar Royal College ta bayar a wata mujallar da ta fitar da farkon makon ranar shayarwa ta duniya, sun kuma hada da;

Ministoci su saka dokoki da zai ba iyaye mata wani wajen kebewa domin damar shayarwa a wajen aiki.

Samar da masu taimakawa mata a lokacin shayarwa.

Hukumar kiwon lafiya al'umma ta Ingila ta kirkiro wasu tsare-tsare domin sauya halayyan mutane wajen shayarwa.

Jami'ar ta kuma bai wa gwamnati shawara sake dawo da wani bincike kan shayarwa a Birtaniya da ake soke a shekarar 2015, wato Uk-wide Infant Feeding Survey.

Kashi 34 kacal cikin 100 na yara ke samun ruwan nono cikin wata shida a Birtaniya, idan aka hada da kashi 49 cikin 100 na yara a Amurka, da 71 cikin 100 na yara a kasar Norway.

Jami'ar Royal College ta ce ta fito da wani bincike da kungiyar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef ta yi, da ke cewa ko da ana shayarwa kadan-kadan ne, zai iya alkintawa hukumar lafiyar Birtaniya wato NHS, da fan miliyan 40 duk shekara, wajen kula da marasa lafiya.

Labarai masu alaka

Karin bayani