Jam'iyyar APC ta yi wa Ganduje tutsu

Haruna Doguwa (na farko a dama) ya ce an kira shi ta waya ne domin ya halarci taron

Asalin hoton, APC

Bayanan hoto,

Haruna Doguwa (na farko a dama) ya ce an kira shi ta waya ne domin ya halarci taron

Uwar jam'iyyar APC ta kasa a Najeriya ta shammaci gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda ta gayyaci mutumin da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso wurin taronta da mukaddashin shugaban kasa.

Umar Haruna Doguwa, wanda ya je wurin taron, shi ne mutumin da ke ikirarin shugabantar jam'iyyar a jihar Kano, kuma mai goyon bayan Rabiu Kwankwaso ne.

Sai dai Abdullahi Abbas, wanda ke goyon bayan Gwamna Ganduje ya sha cewa shi ne halastaccen shugaban jam'iyyar a Kano.

Lamarin dai ya sha jawo ce-ce-ku-ce a jihar, musamman ganin cewa yanzu da dangantaka ta yi tsami tsakanin Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, mutumin da ya yi masa mataimakin gwamna tsawon shekara takwas.

Taron da mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya kira dai ya tattauna ne kan rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a London.

Kazalika, shugabannin jam'iyyar APC na jihohon kasar da suka halarci taron sun bayyana gamsuwarsu da irin ayyukan da mukaddashin shugaban ke yi wa kasar da kuma jam'iyyarsu, tun bayan ficewar Shugaba Buhari daga kasar zuwa London ind ya ke jinya.

A hirarsa da BBC bayan taron, Umar Haruna Doguwa, ya ce "an gayyace ni taron ne kamar yadda aka saba gayyata ta a matsayina na zababben shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.

An kira ni ta waya ne aka gaya min. Muna da tsari na gayyanta inda ake sa wa daya daga cikin shugabannin jam'iyya ya kira mu taron".

Da alama dai wannan gayyatar da APC ta yi wa Umar Haruna Doguwa za ta tayar da jijiyar wuya a tsakanin 'yan jam'iyyar da ke Kano.