Nigeria: Kun san halin da tsadar kayan abinci ta jefa jama'a?

Wata kasuwar kayan abinci a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsadar kayan abincin ya sa jama'a da dama musamman masu karamin karfi komawa yin barace-barace

Jama'a musamman masu karamin karfi a Nigeria na kokawa kan tsadar kayan abinci duk kuwa da saukar damina a kasar, inda da dama suka shiga yawon barace-barace.

Wannan na zuwa kwanakki kadan bayan da hukumar kididdiga ta kasar ta tabbatar da tashin farashin kayan abinci a kasar.

Wani mai sayar da kayan miya ya shaida wa wakilin BBC cewa farashin karamin bokitin fenti na tumatir yanzu Naira dari shida, kana tattasai Naira dari biyar, kwando kuma Naira dari shida ya kama, wanda ya ce duka farashin su sun ninka fiye da na da.

Haka ma batun yake a bangaren masu sayar da naman miya, inda wani mahauci shi ma ya bayyana cewa yanzu kilon naman ya kai Naira dubu daya da dari uku, amma a baya ana sayar da shi Naira dari tara zuwa dubu biyu.

Mahaucin ya kuma kara da cewa; '' Duk da haka wasu suna saye hakan, amma da dama suna kokawa da cewa ya yi tsada.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mahauci ya shaida wa BBC cewa yanzu kilo daya na nama ya kai Naira dubu daya da dari uku ba kamar a baya ba da ya ke dari tara

Wasu magidanta da suka tattauna da BBC sun ce tsadar kayan abinci na shafar rayuwar iyalinsu matuka.

Daya daga cikinsu ya bayyana cewa yanzu haka mutane da dama sun koma barace-barace, ya kuma kara da cewa;

''Taliya kwalinta Naira dubu biyu amma yanzu ya kai dubu hudu har da dari biyar, shinkafa kuma a da za ka samu karamin kwano dari uku da hamsin, amma yanzu ta kai dari shida''.

Magidancin ya kuma ce haka nan dai suke daurewa su samu dan abin da za su ci ko da ba sau uku a rana ba.

''Gaskiya kayan abinci sun yi tsada, muna fata Allah ya yi mana rangwame'', in ji wani dattijo.

Ya ce abin da kamar talaka zai ci kamar su dawa, da gero, da masara ba, kuma sun din ma farashinsu ya ninka.

Labarai masu alaka