Me ye illar sa hotunan iyalanku a shafukan sada zumunta?

Hoton uwa da 'yar ta na salon selfie Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu iyayen sun ce suna wallafa hotunan kananan 'ya'yansu, wadanda za su ji dadi idan sun ga hakan

Wani bincike da hukumar da ke sa ido kan sadarwa a Birtaniya ta gudanar, ya gano cewa iyaye na da ra'ayoyi mabambanta kan ko ya kamata su wallafa hotunan 'ya'yansu a shafukan sada zumunta.

Rahoton da Ofcom ta gabatar, ya nuna kusan kashi 50 cikin 100 na iyayen da ta tattauna da su sun ce suna gujewa yada hotunan 'ya'yansu, ko hotunan iyalai baki daya a shafukan sada zumunta na zamani.

Yawancin iyayen sun ce suna daukar matakin ne, don kare hakkin yaran da ba su kai shekara 18 ba.

Amma wasu daga cikin iyayen, sun ce su kan wallafa hotunan 'ya'yansu sau daya ko biyu a wata.

An wallafa wannan kididdiga ne a mujallar da Ofcom ke fitar wa a duk wata, sun kuma yi amfani da sakamakon binciken da suka yi a shafukan sada zumunta na mutane 1,000 a watan Afirilu da ya wuce.

Hukumar Ofcom ta ce, yada hotunan iyali ko hoton bidiyo a shafukan sada zumunta ba bakon abu ba ne, kamar yadda mutane suka saba da cin abinci.

Daraktan hukumar Lindsey Fussell ya shaidawa BBC cewa, ''Iyaye suna da ra'ayoyi daban-daban kan batun wallafa hotunan 'ya'yan nasu. Abin farin cikin shi ne kusan kashi 80 cikin 100 na iyayen da suke wallafa hotunan suna da kwarin gwiwar cewa abin da suka yi daidai ne, kuma ba su sanya 'ya'yansu cikin hadari ko barazana ba, kuma ba wani abin damuwa ba ne idan aka ga hotunan.''

Misalin irin hotunan da ake dauka na 'yan uwa da abokan arziki musamman idan sun kawo ziyara da sauransu.

Haka kuma kashi 87 cikin 100 sun ce suna bukatar sirri don haka ne ba za su wallafa hotunan ba, yayin da kashi 38 cikin 100 sun ce 'ya'yansu ba sa son su wallafa musu hotunansu haka nan.

Sai dai wasu kashi 57 cikin 100 sun ce 'ya'yansu na jin dadin hotuna har ma da bidiyon da iyayensu ke wallafawa a kansu musamman ma na zamanin kuruciya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yawancin iyayen sun ce suna adana hotunan

Wasu iyayen dai na cewa suna wallafa hotunan ba tare da karanta sharudda da ka'idojin da shafukan sada zumuntar ke sanyawa ba, wasu kuma sun ce abu ne mai wuya ka iya goge hotunan matukar ka wallafa su.

Wata kungiyar bai wa kananan yara agaji ta yi kira ga iyaye su yi taka tsantsan din wallafa hotunan 'ya'yansu.

Mai magana da yawun kungiyar NSPCC ta ce, ''a duk lokacin da aka wallafa hotunan da bidiyo suna barin wani tabo da zai bibiyi yara har girmansu, ya danganta da yanayin hoton. Yana da matukar muhimmanci a tambayi yaran kafin a wallafa su.''

A cewar ta ''Ya kamata ka san ko idan ka wallafa irin hotunan za su sanya yaran farin ciki ko akasin haka, don haka idan ka tambayi izininsu ba laifi ba ne.''

Salon daukar hoton dauki da kanka ko Selfie

Bincike ya kuma fadada, don gano ko mutane na jin dadi idan aka wallafa hotunansu ko akasin hakan.

Binciken ya gano cikin hotuna da mutane suke wallafawa nasu, kusan rabi da kansu suka dauka, a salon na dauki da kanka.

Haka kuma, yanayin yadda mutane ke amfani da shafukan sadarwa na Instagram, da Snapchat da Facebook, sun sanya mutane na bata minti daya ko biyu su sake yi wa hoton da suka dauka kwaskwarima kafin su wallafa, misali kara hasken hoto, ko cire jan abun da ke cikin ido da sauransu.

Ba nan binciken ya tsaya ba, ya sake duba ko yaya mutane suke ji a kan hotunansu da suka wallafa da na wasu: kashi 61 cikin 100 sun ce hotunan da suka wallafa nasu ba su yi masa kwaskwarima sosai ba, yayin da kashi 74 su kan kwaskware hotunan sosai.

Shafukan sada zumunta na Facebook da YouTube

Wasu rahotannin sun ce a daidai lokacin da matasan Birtaniya sama da miliyan 42 da suke ziyartar shafin Youtube don kallon bidiyo, shi kuwa shafin Facebook mutane miliyan 39 da dari bakwai ne suke bibiyar shi.

Daga bisani kuma sai adadin ya rubanya, idan aka kwatanta da lokacin bazara na bara lokacin da hukumar sa ido kan harkokin sadarwar zamani ta yi bincike ta kuma gano sama da mutane 12,00 ne suka yi amfani da shafukan kuma masu amfani da wayoyin komai da ruwanka.

Wasu abubuwan da binciken ya gano sun hada da:

  • An samu raguwar masu amfani da masu na'urar sadarwa ta tablet, duk da binciken ya ce lamarin ka iya sauyawa.
  • Kusan kashi 40 na mutane kasa da shekara 55, sun mallaki akwatin talabijin mai amfani da internet. Ko dai saboda wasannin game da yara kan yi, ko don saukaka kashe kudi a internet.
  • Kashi 9 cikin wadanda binciken ya tattauna da su, sun ce yawanci sun fi jin dadin kallo a bandaki, ko a lambun cikin gida da sauransu.
  • A shekarar da ta wuce kafar sadarwa ta Snapchat to fi kowacce farin jini tsakanin matasa.
  • Haka kuma kashi 88 na manya su na iya amfani da internet a gida, yayin da kashi daya ne kacal na wadanda ba su iya amfani da shi ba ke amfani da intenet a shekarar nan.