Barayin gashi sun addabi matan karkara a India

Sunita Devi kenan tsaye a kofar gidan ta
Image caption Sunita Devi ta ce ta shiga matukar damuwa bayan sace mata gashi

Fiye da mata 50 da ke zaune a arewacin jihohin Haryana da Rajasthan ne, suka yi korafin an yanke musu gashin kai bayan an sanya sun fita daga hayyacinsu.

'Yan sanda na fadi tashin gano bakin zaren wanda ya bar mata cikin halin zullumi da dimuwa, kamar yadda wata mace da lamarin ya rutsa da ita ta shaida wa BBC.

Matar mai suna Sunita Devi mai shekara 53, kuma matar aure da ta fito daga yankin Bhimgarh Kheri a gundumar Gurgaon da ke Haryana, ta ce ta shiga dimuwa da tashin hankali a lokacin da aka yanke mata gashi.

Ta ce a ranar Juma'a da ta wuce ne lamarin ya faru, bayan ta farfado ta ga yadda aka yanke mata gashin kai sai ta shiga halin dimuwa.

Ta kara da cewa ''Ban iya bacci ba a wannan ranar, na sha jin labarin matan da aka sacewa gashi, amma ban taba zaton abin zai zo kaina ba.''

A farkon watan Yuli ne aka fara kai wa 'yan sanda korafin barayin gashi da suka fara addabar mata a yankin Rajasthan, a hankali kuma sai aka samu rahoton sace gashin a Haryana da birnin Delhi.

Yankin da Sunita ke zaune dai wuri ne kewaye da 'yan kasuwa da manoma, kuma wasu daga cikin makwabtanta sun zo taya ta zama tun bayan afkuwar lamarin saboda firgitar da ta yi.

Ta kara da cewa, ''mutumin da ya kawo min hari tsoho ne, sanye da tufafi mai launuka daban-daban.

"Ina zaune a tsakar gidanmu, da misalin karfe 9.30 na dare, surukata na sama tare da jikana sai kawai na ji kamar an make ni na fita a hayyacina, da na farfado sai na ga an yanke min gashi.

"Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne surukata da jikana ba su ji motsin komai ba, don haka ba su ga mutumin da ya min aika-aikar ba.''

Image caption Munesh Devita ta shaidawa BBC cewa mutane na zaman dar a yankinsu, musamman mata

Ban shiga tashin hankali ba, sai da na tambayi ko sun ga barawon da ya zo har gida ya sace min gashi.

Wata makwabciyar Sunita mai suna Munesh Devi, ta ce daman lungunsu mai dauke da gidaje 20 ya kan yi shiru da tsoratarwa daga karfe 9 na dare zuwa 10.

Ta kara da cewa, ''Mutane kan zauna bayan cin abincin dare a yi ta hira, ko a ranar da abin ya faru mun zauna hira da daren amma ba mu ga wata bakuwar fuska da ta shiga ko fita daga gidan Sunita ba.''

Lamarin ba a nan kadai ya tsaya ba, kwanaki kadan tsakani a nan kusa da gidansu Sunita, wata mace mai suna Asha Devi ta hadu da masu satar gashin matan, amma wannan karon mace ce kuma tsohuwa.

Surukin Asha, Suraj Pal ya shaidawa BBC yadda lamarin ya faru, ''Ina zaune a gida a lokacin da surukata ta fito don karasa ayyukan da take yi kafin kwanciya bacci, lokacin karfe 10 na dare ne.

"Da na ji shiru sai na leka don na ga me take yi, sai na ganta yashe a kasa a cikin bandaki an kuma yanke mata gashi.''

Suraj ya ce dole ta sanya ya tura dukkan matan gida gidan wata 'yar uwarsu da ke jihar Uttar Paradesh, saboda sun firgita matuka.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Birnin Delhi ma bai tsira ba, cikin yankunan da ake sacewa matan gashi

Bayan sa'a guda, Asha ta dawo hayyacinta ta kuma fadawa surukinta wata mace ce ta sanya ta fita daga hayyacinta, kana da yanke mata gashi.

Ta kuma shaida masa abin ya faru ne cikin dakika 10.

Lamarin irin wannan ya faru a wasu kauyukan da ke gundumar Rewari mai nisan kilomita 70 daga Gurgoan.

Wata matashiya Reena Devi, mai shekara 28, daga kauyen Jonawasa ta ce an kai mata hari a makon da ya wuce, ta ce wanda ya sace mata gashin ya yi kama da mage, saboda gabannin abin ya faru da tana wanke-wanke ta ga inuwar wani abu kato kamar mage.

Sai ta ji kamar wani ya taba mata kafada, abin da za ta iya tunawa kenan. Ta amince labarin yadda tata kaddarar ta faru ba mai saukin fahimta ko amincewa ba ne, abin da ta gani ta ke fada.

A kauyen Kharkharra, ma Sundar Devi, mai shekara 60, na cikin halin jiyya ba inda ta ke zuwa saboda tsoro.

''A ranar lahadi tawa kaddarar ta same ni, lokacin da na ke kan hanyar zuwa gidan makofciyarmu, sai wani ya dan dakar min kafada ta bayana amma da na juya baya ban ga kowa ba, abinda zan iya tunawa kenan,'' in ji ta.

Reema Devi, mai shekara 28, ta ce tana zaune a kofar daki inda ta ke buga wasan game a cikin wayar salularta, kawai sai ta ji an yanke mata gashi.

Ta kara da cewa, ''Mijina da 'ya'yana suna cikin dakin a lokacin da abin ya faru, sai na ji kamar an ja min gashi, ina waiwayawa sai na ga gashina yashe a kasa.''

'Camfi'

Mai magana da yawun 'yan sandan yankin Gurgaon Ravinder Kumar, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce lamarin mai cike da sarkakiya ne, don safai ake ganin ya faru ba, abin damuwar shi ne babu wata alama da jami'an tsaro suka gani a wuraren da abun ya faru.

Haka kuma gwaje-gwajen da likitoci da kwararru suka gabatar kan matan da aka sacedwa gashin bai nuna komai ba.

Mista Kumar ya ce ''Wadanda lamarin ya rutsa da su ne kadai suka san abin da ya faru, don haka babu takaimai shaidar da za a dogara da ita ko wata hanya da za ta ba mu hasken ta inda za mu fara binciken, abun akwai tashin hankali gaskiya.''

Image caption Tsohuwa Sundar Devi, mai shekara 60, da aka yanke mata gashi
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu matan na amfani da abin matse gashi mai hoton abin bautarsu, da suke sa ran zai kare su daga barayin gashi

Ana ta yada jita-jita da labarai daban-daban kan batun.

A tafiye-tafiyen da na yi, a kauyukan Indiya na samu karin labarai mabanbanta kan masu sacewa matan gashi,'' in ji wakiliyar BBC, Vikas Pandey.

Wani tsoho a wani kauye ya shaidawa BBC ana zargin wasu gungun masu aikata muggan laifuka da hannu a satar gashin.

Wani daban kuma ya ce bokaye ne ke haddasa hakan saboda bukatar wasu abubuwa da za a ce a yi amfani da su don hada magani.

Yayin da wata mace ta ce, lamarin ya fi kamata da aikin aljanu, wasu matan na cewa wasu mutane da suke son a kula su ne ke aikata hakan.

Amma wasu mazan ba su amince da lamarin ba, sun ce babu wani aljani da ke zuwa ya yanke musu gashin kai, hakan na faruwa ne ga matan da suka samu kansu a ciki na halin kunci ko damuwa dalili kenan da suke ganin kamar wani ne ya sadado tare da yanke musu gashin.

Sai dai matashiya Reena Devi ba ta amince da hakan ba.

"Na shafe shekaru masu yawa ina tattalin gashina, kuma idan na kalle shi ta madubi ina jin dadi.

"Ba ku san yadda na ke ji ba a yanzu da babu gashin, abin yana matukar kona min rai, don haka ban amince wai da kanmu muke yanzke gashinmu ba.'' in ji ta.

Karin wasu camfe-camfen a Indiya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
  • A tsakiyar shekarun 1990, miliyoyin mabiya addinin Hindu a sassa daban-daban na duniya sun yi mamaki da al'ajabin rahotannin wasu gumaka da ake bautawa na shan madarar da aka kai wurin bautar sadaka.
  • Haka a shekarar 2001 aka samu rahoton wani Biri da ke tare mutane a Delhi, shi ma an sanya shi cikin batun camfe-camfe.
  • A shekarar 2006 kuma dubban mutanen Indiya daga sassan kasar ke yin tattaki har zuwa birnin Mumbai don ganewa idanunsu wata jita-jitar da aka yada wai babban kogin da ke gudana ya sauya dandano zuwa na sikari.

Labarai masu alaka