Ana farautar wanda ya kashe maguna a Saudiyya

Asalin hoton, Twitter
Mutumin wanda ya bayyana a cikin bidiyon amma fuskar ta kasance a rufe
Hukumomin a Saudiyya suna farautar wani mutum wanda ake zargi da kashe maguna da dama a kasar.
An kaddamar da binciken ne bayan wani faifan bidiyo ya bayyana a kafofin sada zumunta wanda yake nuna wani mutum ya harbe wasu maguna a birnin Jeddah.
Hukumomin kasar sun ce suna nemansa ruwa a jallo.
Bidiyon wanda aka wallafa a shafin sada zumunta na Snapchat ya nuna wani mutum rike da bindiga yana bin unguwanni yana kashe maguna.
Hakan ya sa mutane da dama sun bayyana damuwarsu a kafofin sada zumunta, yayin da wasu suka bukaci a binciki al'amarin.
Bidiyon ya nuna daya daga cikin magunan tana shure-shuren mutuwa bayan an harbe ta.
Mutumin wanda ya bayyana a cikin bidiyon amma fuskarsa ta kasance a rufe.
Ba a dai bayyana sunan mutumin ba tukuna. Hakazalika ba a san abin da ya sa shi yin hakan ba.
Ba wannan ba ne karon farko da aka taba samun kashe-kashen mage ba.
Don ko a watan Yuni an sanyawa wadansu maguna 200 guba a abinci a kauyen Saint Pierre la Mer na kasar Faransa.
Hakazalika, a watan Yuli an yanke wa wani mutum a jihar California ta kasar Amurka hukuncin dauri shekara 16 bayan da ya amsa laifin azabtarwa da kuma kisan wasu maguna 18.