Buhari ya yi wa gwamnan Osun Rauf Aregbesola waya

Ana sa ran shugaban zai koma gida nan ba da dadewa ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana sa ran shugaban zai koma gida nan ba da dadewa ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wo gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola ta wayar tarho inda ya yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Saratu Aregbesola.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twiiter ta ce Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a London, ya yi wayar ne ranar Alhamis.

Ya kara da cewa shugaban ya yi addu'ar Allah ya jikan Saratu Aregbesola.

A cewar sanarwar, shugaban na Najeriya ya bayyana marigayiyar a matsayin "mace mai kwazo wacce ta kasance katanga ga 'ya'yanta.''

A watan jiya ma, Shugaba Buhari ya yi wa tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar Cif Bisi Akande wayar tarho, inda ya yi masa ta'aziyya a kan rasuwar matarsa Madam Omowunmi Akande.

A watan jiya ne mukaddashin shugaban kasar da wasu gwamnoni da kuma shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar suka ziyarce shi a London, inda suka ce yana samun sauki.

A watan Yunin shekarar 2016 ne shugaban, mai shekara 74 a duniya, ya soma tafiya London domin yin jinyar abin da, a wancan lokacin, jami'an gwamnati suka bayyana da ciwon kunne.

A farkon wannan shekarar ma Shugaba Buhari ya koma London inda aka duba lafiyarsa.

A lokacin da ya koma kasar a watan Maris, ya ce an yi masa karin jini, ko da yake bai fadi larurar da yake fama da ita ba.

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce bai taba yin jinya irinta ba a rayuwarsa.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London
 • 22 ga watan Yuli - Wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar sun gana da shi
 • 24 ga watan Yuli - Karin gwamnoni, ciki har da na PDP - sun ziyarci Buhari