Shugaban Cocin Ingila ya ziyarci Shugaba Buhari

Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Gwamnonin sun ce sun samu Shugaba Buhari cikin raha, kamar yadda ya saba.

Shugaban Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby, ya kai ziyara ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Landan.

Justin Welby ya ziyarci Shugaba Buhari ne, wanda ya kwashe kusan wata uku yana jinya a birnin Landan ranar Juma'a.

"Na yi farin ciki kan yadda na ga Buhari ya murmure cikin sauri," in ji jagoran cocin.

A baya ma dai jagoran cocin ya kai ziyara ga shugaban, lokacin da ya yi jinya a farkon shekarar nan.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar ke jinya a Ingila a shekarar 2017.

Ya fice daga kasar ne ranar bakwai ga watan Mayun jim kadan bayan ya gana da 'yan matan Chibok 81, wadanda aka sako a makon da ya bar kasar.

A watan Yunin shekarar 2016 ne shugaban, mai shekara 74 a duniya, ya fara tafiya Landan domin yin jinyar abin da, a wancan lokacin, jami'an gwamnati suka bayyana da ciwon kunne.

A farkon wannan shekarar ma Shugaba Buhari ya koma Landan inda aka duba lafiyarsa.

A lokacin da ya koma kasar a watan Maris, ya ce an yi masa karin jini, ko da yake bai fadi larurar da yake fama da ita ba.

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce bai taba yin jinya irinta ba a rayuwarsa.

A watan jiya ma, mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Buhari, inda ya ce yana samun sauki sosai.

Su ma wasu gwamnonin kasar, ciki har da na jam'iyyar PDP mai hamayya da kuma shugaban jam'iyyar APC, sun gana da shugaban.

A cewar shugaban kungiyar gwamnonin APC, Rochas Okorocha, nan ba da dadewa Shugaba Buhari zai koma gida.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London
 • 22 ga watan Yuli - Wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar sun gana da shi
 • 24 ga watan Yuli - Karin gwamnoni, ciki har da na PDP - sun ziyarci Buhari

Labarai masu alaka