Shin ya kamata masu nakasa su rika barace-barace?

Wasu guragu na wasan kwallo a Nijeriya
Image caption Wasu masu nakasar na kyamar sana'ar barace-barace

A kasashe masu tasowa kamar Najeriya, wasu nakasassu kan yanke kauna da yin wata sana'a ko karatun zamani, a maimakon haka su kan kama barace-barace.

To sai dai akwai masu nakasar da suke kyamatar al'adar barace-baracen su shiga yin sana'o'a daban-daban.

Wasu ma kan yi karatun zamani kamar takwarorinsu masu lafiya, har ma su shiga gogayyar neman aiki da su.

Mathew Micheal Dibale, wani gurgu ne a birnin Abuja, da yake kai-komo tsakanin ma'aikatu domin neman aiki, ya kuma shaida wa BBC cewa ya kammala karatu har ya samu babbar diploma a makarantar Kimiyya da Fasaha ta jihar Plateau a farin Barikin Ladi.

'' Na gama makaranta har na yi bautar kasa, na kuma yi karatu ne a fannin aikin ofis, na kammala aikin bautar kasa a shekara ta 2012 zuwa 2013'', in ji Mathew.

Image caption Nakasassu da dama a kasashe masu tasowa kan yanke kauna ga sana'ar ta dogaro da kai su rika barace-barace

Mr. Mathew ya ce bai ga dalilin da zai sa ya shiga sana'ar bara ba; ya tsaya a hanya yana roko, don haka ya yi tunanin neman ilmin zamani don ya taimaki kansa da iyalinsa.

Ya kuma ce yana bukatar gwamnati ta taimaka masa da abin yi wanda zai taimaki kansa tun da ba noma zai iya yi ba.

'' Saboda lalura na zama gurgu ba zan iya noma ba, amma idan na samu aikin yi zan ji dadi.''

Bayan da ya gama makaranta in ji Mathew, ya fara da koyon gyaran keke, amma an wayi gari yanzu babu keke a babban birnin tarayya Abuja, da ma wasu biranen.

Ya kuma kara jaddada cewa sana'ar barace-barace aba ce wanda sam bai yarda da ita ba, inda ya ce ya fi son ya dogara da kan sa, shi yasa ma ya koma karatu.

'' Idan gwamnati za ta taimake ni da jari zan iya bude wajen buga takardu da sauransu, yadda zan rika samun kudin shiga ba tare da tunanin yin wata bara ba.''

Labarai masu alaka