Wadanne 'yan wasa ne Madrid da Man Utd ke son saya?

Mbappe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kylian Mbappe na cikin 'yan wasan da manyan kugiyoyin kwallon kafa na Turai ke nema ruwa a jallo

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi amannar cewa wajibi ne kulob dinsa ya sayar da Gareth Bale, idan har za su sayi dan wasan gaban Monaco Kylian Mbappe, a cewar jaridar Marca.

Daily Star ta ruwaito cewa Manchester United tana nazari kan abubuwan da ke faruwa a Madrid kuma ta shirya zawarcin dan wasan tawagar Wales Gareth Bale kan kudi fam miliyan 90 (kimanin naira biliyan 43 ke nan).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gareth Bale dai ya ce yana jin dadin wasa a Madrid

Amman Kocin United, Jose Mourinho, ya kafe cewa ba zai sayi Bale a kan abin da ya kai fam miliyan 90 (kimanin naira biliyan 43 ke nan) in ji jaridar Daily Express.

Jaridar Independent cewa ta yi dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, zai mika wasikar neman barin kungiyar.

Lauyan Costa ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan Chelsea bayan kungiyar ta kafe kan sai ya tafi AC Milan a bashi kafin ya koma tsohuwar kungiyarsa wato Atletico Madrid, bayan an dage takunkunmin cinikin 'yan wasa ga kungiyar kwallon kafar Spain a cewa jaridar Mirror.

Zakarun Faransa, Monaco, suna shirin taya dan wasan gaban Arsenal, Alexis Sanchez, wanda kwantiraginsa da kungiyar ta shiga shekarar karshe, kan fam miliyan 45 (kimanin naira biliyan 21), a cewar The Sun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Arsenal Arsene Wenger dai ya ce Sanchez zai ci gaba da murza leda a kungiyar

Tottenham na zawarcin dan wasan gaban Genoa, Giovanni Simone, in ji Mirror.

Har yanzu Kocin Everton Ronald Koeman, yana fatan zai sayi karin dan wasan gaba a lokacin bazarar nan yayin da yake tunanin neman dan wasan gaban Arsenal Oliver Giroud, mai shekara 30, kamar yadda Liverpool Echo ta bayyana.

Mai tsaron bayan kungiyar Southamton, Virgil van Dijk, zai iya kasa buga wasan farko a Gasar Firimiya a wannan kakar yayin da makomarsa ke cike da tababa, in ji Telegraph.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Van Dijk ya koma Southampton daga Celtic a shekarar 2015

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shirya kalubalantar Liverpool kan Van Dijk bayan ta taya shi a kan fam miliyan 50 (fiye da naira biliyan 24 ke nan) in ji jaridar The Times.

Ita kuwa Sunderland ta shirya domin sayar da Jeremain Lens, bayan cimma yarjejeniya kan fam miliyan 4.5 (kimanin naira biliyan biyu) da kungiyar Besiktas, kamar yadda Sunderland Echo ta bayyana.

Labarai masu alaka