Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Fitattun hotunan abin da ya faru a Afirka da sauran sassan duniya a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bikin raye-raye da wake-wake na duniya da ake yi duk shekara, inda kungiyoyin suka zo daga kasashen Morocco da kuma Algeria ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ivory Coast ce ta karbi bakuncin gasar wasannin kasashe renon Faransa , wanda ta fi mayar da hankali kan wasannin gargajiya da al'adu, Debe Blaise na kasar Burkina Faso ne (daga dama), da Garba Mourtala na jamhuriyar Nijar a karawar da suki a demben kusa da karshe a ranar Alhamis.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bikin bude sabon sansanin sojin ruwan kasar China na farko a kasar Djibouti wanda aka yi ranar Talata. Hukumomin kasar China sun karyata zargin cewa Chinan na kara fadada karfin sojinta, inda ta ce ta girke sansanin ne saboda dalilai na tsaro. Wanda zai taimaka wa jiragen ruwan da ke zirga-zirga a yankin gabashin Afirka, da kuma tabbatar da zaman lafiya, tare da ayyukan agaji.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata tankar yakin Angola ke nan ke atisaye a kusa da birnin Moscow a karshen makon jiya...Amma a zahiri ba harbi take yi ba, kawai tana wasa ne a wani bangare na gasar wasan sojoji na shekarar 2017.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadansu sojojin kasar Masar suna daukar kansu a hoto kafin fara wasan kwallon kafa da za a kara tsakanin ES Tunis da Al Hilal lokacin gasar cin kofin zakarun Larabawa a birnin Alexandria ranar Lahadin da ta gabata.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan adawa yayin da suka fito bakin titunan Conakry babban birnin Guinea ranar Laraba, don nuna adawarsa a akan kin yin zaben kananan hukumomi bayan shekara 12.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yayin da ke gab da kara zaben Kenya, mutane da dama sun barin babban birnin kasar Nairobi don komawa garuruwansu saboda su kada kuri'arsu a can kuma suna tsoron tashin hankali bayan zabe.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bikin kammala gasar wasannin kasashe renon Faransa da aka yi a Ivory Coast a ranar Lahadi, wanda kusan mutum 3,000 suka shiga gasar.

Labaran BBC