Rwanda: Kagame yar lashe zaben shugaban kasa babu hamayya

From left to right: Paul Kagame, Frank Habineza and Philippe Mpayimana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Paul Kagame (Hagu), Frank Habineza (Tsakiya) da Philippe Mpayimana (Dama)

Hukumar zaben kasar Rwanda ta ce shugaba Kagame yayi nasarar zama shugaban kasar a karo na uku.

Hukumar ta ce sakamakon zaben da ta kirga kawo yanzu ya ba shugaban mai ci kashi 98 cikin dari na kuri'un.

Magoya bayan Mista Kagame sun fito titunan kasar suna nuna murnasarsu gabanin bayyana sakamakon da hukumar zaben tayi.

Hukumar zaben kasar ta ce kashi 97 cikin dari na masu kada kuri'a ne suka fito, a cikin masu kada kuri'a miliyan 6.9 da hukumar zaben ta yi wa rajista.

'Yan takara uku ne suka fafata da shugaba Kagame, wadanda suka hada da Frank Habineza na jam'iyyar Democratic Green Party ta Rwanda da Philippe Mpayimana dan takarar mai zaman kansa.

Gyaran da aka yi wa tsarin mulkin kasar a shekarar 2015 ya ba Kagame damar tsayawa zabe a karo na uku, kuma yana iya cigaba da mulkin kasar har shekara ta 2034.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paul Kagame ya lashe zaben shugaban kasar shekarar 2010 da kashi 93 cikin dari na kuri'un da aka kada

Game da Paul Kagame

Paul Kagame ya lashe zaben shugaban kasar shekarar 2010 da kashi 93 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Wasu na ganinsa a matsayin kwararren gwarzon mayaki.

Sojojin da ya shugabanta sun taimaka wajen dakile rikicin kabilancin shekarar 1994 - kuma tun lokacin yake kan karagar mulki.

Sau biyu yana kai wa makwabciyar kasar Congo hari.

An sha tuhumarsa da hana 'yan adawa sararin motsawa, da kuma hallaka masu sukar gwamnatinsa.

Mai kallon kasashen Singapore da Koriya ta Kudu a matsayin ababen koyo - tattalin arzikin Rwanda na habaka a kashi 7 cikin dari a kowace shekara.

Mai girmama 'yancin mata ne: yawancin 'yan majalisar kasar Rwanda mata ne.