Adikon Zamani - Tattaunawa kan mata da shan kayan maye
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Mijina ke sa ni shan Codein kwalba 10'

  • Akwai cikakkiyar zantawar da Fatima Zarah Umar ta yi da likitan kwakwalwa da wata mai fafutuka kan amfani da miyagun kwayoyi, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Sunan da aka fi saninta da shi a duniyar bariki shi ne Baby yo.

Ta kura min ido kur cike da zargi. Muna gaban kantin sayar da kayan kwalam na Drumstick da ke titin Aminu Kano a unguwar Wuse II, da ke babban birnin Najeriya Abuja.

Na ja ta muka nufi wajen mota don ta nuna min kayan shagalin nata kamar yadda take cewa, wanda ba komai ba ne sai tulin kwayoyin sa maye kamar su wiwi da kwalaben maganin tari irinsu Codeine, da kuma manyan irin su koken.

Sai na tambaye ta nawa ta sayi kayan? Ai ko caraf sai ta ce naira dubu 100.

Titin Aminu Kano matattara ce ta 'yan kwaya, inda da safe za a gan su suna rara-gefe don neman abin da za su kai bakin salatinsu da kuma kayan mayen da za su afa bayan sun gama baje-kolinsu da daddare.

Ire-iren Baby yo suna da yawa a arewacin Najeriya. A birane da garuruwa da kauyuka da dama shaye-shayen kayan maye ya zama ruwan dare musamman a tsakanin mata, kuma abin takaicin shi ne yadda muke kin mayar da hankalin kan batun.

A matsayinmu n al'umma mun fi mayar da hankali wajen yanke wa masu yi hukunci fiye da nemar musu mafita. A yanzu haka muna asarar mata da yawa wadanda a maimakon su zama masu amfani da za a yi alfahari da su, sai suke rikidewa suna zama 'yan kwaya.

Me ya sa mata da dama ke kara zama 'yan maye? Me ya sa suka mayar da shan kayan maye wasu abubuwan warkar musu da matsaloli?

Wasu matan dai sun ce matsalolin gidan aure ne suka zama sanadinsu na fara shan kayan maye.

Wata baiwar Allah mai suna Mariya (ba sunanta na gaskiya ba), ta ce mijinta na yawan bakanta mata rai, sai kawai ta gane hanya mafi sauki wajen kawar da bakin cinkinta ita ce ta kwankwadi kwalaben codeine 10.

Ita kuwa wata matashiya da ita ma ta ce kar na ambaci sunanta, ce min ta yi duk lokacin da suka yi fada da matar babanta to ba ta samun nutsuwa sai ta sha kwalba 10 ta codeine.

Haka dai mafi yawan 'yan matan ke samun kansu cikin wannan yanayi. Abin takaicin shi ne yadda suke kara dulmiyewa amma babu mai yin wani hobbasa cikin al'umma don dakatar da hakan.

Yara mata kan fara shan kayen maye tun suna shekara 12 amma ba a farga da hakan sai lokaci ya kure.

Iyaye ba su cika yarda cewa 'ya'yansu na wannan halayya ba, shugabannin al'umma kuma sun yi shiru. Wasu daga cikin mutanen da na zanta da su sun ce min iyaye sun gwammace su zargi makiyansu maimakon su tunkari 'yan'yan nasu kan batun.

Me ya sa haka? Me ya sa iyaye ba sa tunkarar 'ya'yansu kan wanann batu? Yaushe muka mayar da dabi'ar shan kayan maye ta zama kamar ba laifi ba a al'ummarmu?