Ra'ayi: Wane irin tasiri komawar manyan hafsoshin soji Maiduguri za ta yi?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Wane irin tasiri komawar manyan hafsoshin sojin Najeriya Maiduguri za ta yi?

Hafsoshin sojin Najeriya sun koma birnin Maiduguri na Najeriya don yaki gwa-da-gwa 'yan Boko Haram. Sun yi hakan ne bisa umurnin Mukaddashin Shugaban Najeriyar, Yemi Osinbajo, bayan kisan malaman jami'a da wasu kwararrun ma'aikatan da ke binciken man fetur a yankunan tabkin Cadi. Wane mataki ya kamata sojin su dauka wanda ya sha bamban da wadanda suka dauka a komawa Maidugurin da suka taba yi a baya? Ko kwalliya za ta biya kudin sabulu kuwa? Wadannan suna cikin batutuwan da muka tattauna a wannan makon, a filinmu na Ra'ayi Riga.