Hotunan abin da ya faru a Nigeria makon jiya
Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT
Mutum 40 da ake zargi da satar mutane don neman kudin fansa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna yayin da rundunar 'yan sanda ta gabatar da su ga manema labarai a makon jiya.
Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT
Wasu daga cikin gwamnonin arewacin Najeriya yayin da suke taro a Kaduna makon jiya.
Asalin hoton, APC
Wadansu mambobin jam'iyyar APC daga jihar Kano bayan sun gana da Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da Shugaban jam'iyyar APC John Oyegun ranar Alhamis.
Asalin hoton, LAGOS STATE GOVERNMENT
Mutum 28 da ake zargi da aikata luwadi yayin da aka gurfanar da su a gaban kotun majistiri da ke unguwar Yaba a jihar Legas ranar Laraba.
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby, yayin da ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a Landan ranar Juma'a.
Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT
Mambobin kwamitin sake fasalin jam'iyyar APC yayin da suke ganawa ranar Asabar.