Nigeria: An kashe mutum 11 a coci

Wasu 'yansandan Nigeria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kusan shekaru biyu ke nan ana kai ruwa rana tsakanin jami'an tsaro da kungiyar

Akalla mutum 11 ne suka mutu bayan wasu 'yan bindiga sun kai wani hari a wata coci da ke jihar Anambra a kudancin Najeriya, kamar yadda rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Garba Baba Umar ya ce al'amarin ya faru ne a cocin St Phillip's Catholic Church, na garin Ozubulu da ke yankin karamar hukumar Ekwusigo.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa 'yan bindigar sun kai hari cocin ne da misalin karfe 5:45 na safe.

Ya ce "bayan sun shiga cocin sai suka fara harbi kan mai uwa da wabi, yayin da masu ibada kowa ya yi ta kansa. Mutane da dama ne suka jikkata."

Sai dai kawo yanzu ba a san dalilin kai harin ba tukuna.

Kafafen yada labarai a kasar sun ce mutane da dama sun mutu yayin da ake kokarin kai su asibiti.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu 'yan asalin yankin ne suka kai harin.