'Son zuciya ne ya hada El-Rufa'i da Shehu Sani a Kaduna'

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Jam'iyyar ta rabu gida ne a jihar wato bangaren APC akida da kuma bangaren Gwamna el-Rufa'i

A kwanakin baya ne kungiyar 'yan jarida ta Najeriya NUJ ta yi Allah-wadai bisa wani hari da wasu 'yan dabar siyasa suka kai a sakatariyar 'yan jarida da ke Kaduna yayin wani taron manema labarai.

Wasu yan majalisar dattijan jihar ne suka kira taron manema labarai domin nuna damuwa a bisa yadda al'amura a jami'ar APC ke tafiya.

Manyan 'yan siyasar jihar sun zargi gwamnatin jihar da shirya harin, sai dai gwamnatin ta musanta zargin kuma ma har Allah-wadai ta yi da wadanda suka kai shi.

Sanata Shehu Sani, wanda ya raba gari da bangaren Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i, ya ce abin da ya sa suka kira taron "shi ne yau ga shi abin da muke sukar PDP da shi mun koma muna yi. Ana shiga daki a rubuta sunaye ana tsoron a yi zabe. Yau ga shi an turo yara su ci mana mutunci. Wannan shi ne siyasa?"

An dade ana samun takun saka tsakanin bangarorin jam'iyyar APC biyu a jihar wato 'yan APC akida da kuma maso goyon bayan gwamnatin jihar.

'Yan APC akida suna zargin gwamnatin jihar da kin cika alkawuran da ta daukar wa jama'a, yayin daya bangaren kuma yake musanta zargin.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Sanata Shehu Sani shi ne ya fara raba gari da gwamnan

Akwai wadanda suke tsoron cewa al'amarin zai jawo cikas ga zabukan kananan hukumomi da jihar za ta yi.

Me ya jawo baraka a APC a jihar Kaduna?

Akwai masu sharhin da suke ganin cewa ricikin ya samo asali ne tun lokacin da kafa jam'iyyar APC a jihar Kaduna, kamar yadda Dokta Tukur Abdulkadir na Jami'ar jihar Kaduna (KASU).

Ya ce: "'Yan siyasar da suke wannan takaddamar sun fito ne daga jam'iyyu daban-daban. Akwai tsoffin wadanda suka yi PDP da CPC da ANPP. Rashin yarda da junansu ne ya haddasa wannnan barkar a jam'iyyar a jihar."

"Abu na biyu da ya jawo rikicin shi ne rashin hakuri daga kowane bangare," in ji shi.

Har ila yau, ya ce yadda gwamnatin tarayya ta ba da mukamai ya kara rura wutar rikicin, inda ya ba da misali da yadda wasu 'yan jam'iyyar suka rika korafi kan "yadda aka bai wa wata wadda ba a santa a jam'iyya ba mukamin minista daga jihar Kaduna."

Ya ce hakan ya kara raba kan jam'iyyar musamman yadda wasu suke "ganin wadda aka bai wa mukamin tana da alaka da shi gwamnan jihar."

Rikicin ya fara ne tsakanin Gwamnan El-Rufa'i da Sanata Shehu Sani 'yan watanni bayan kammala zaben shekarar 2015, amma daga bisani sai ya bazu inda sauran manyan 'yan siyasar jihar kamar Sanata Suleiman Hunkuyi da tsohon dan takarar kujerar gawamna a jam'iyyar CPC Haruna Sa'id wadanda ake kallon suna tare da gawmna amma sai ta bayya ba sa tare.

Doktar Tukur ya ce "idan shugaba ya kasance yana fada da ko wanne bangare to ka ga za a ce akwai matsala."

"An saba ganin gwamna yana rikici da sanatan ko ministan jiharsa, amma idan kuwa ya kasance bangarori da dama ne suke adawa da gwamnan to ya nuna ba ya ga matsalar kuma kila shi ma gwamna yana da wasu matsaloli nasa."

Ya ce don haka ya kamata gwamnan ya duba kuma ya gyara saboda ci gaban jam'iyyar da kuma nasarar mulkinsa.

Wanne tasiri zai kawo a siyasar jihar?

"A gaskiya zai kawo nakasu ga siyasar jihar," in ji malamin jami'ar.

"A tarihi tun daga jamhuriya ta biyu, babu wani gwamnan da ya samu karbuwa daga kowane bangare na jihar kamar Gwamnan el-Rufa'i. Ka ga irin wannan farin jini zai tabbatu ne kawai idan an kiyaye samun baraka a cikin gida, an kuma kiyaye take hakkin juna," a cewarsa.

Wanne nakasu hakan zai haifar a zaben shekarar 2019?

Ya ce bai dace ko wanne bangare ya rika ganin idan bashi ba to kowa ma ya rasa.

Har ila yau, ya ce hakan zai "iya bai wa jam'iyyar adawa a jihar karin tagomashi kuma zai iya kai ga faduwar jam'iyyar a jihar a zaben shekarar 2019."

"Ya zama wajibi ga dukkan bangarorin su yi hakuri da juna kuma su yi la'akari da bukatun al'ummar jihar, ba bukatun kansu ba."

Zaben kananan hukumomi a Kaduna

Wannan tabbas ne, kamar yadda ya ce.

Ya ce don haka kamata duka bangarorin biyu su yi karatun ta-natsu. "Su yi hakuri da juna," in ji shi.

Ta wace hanya za a warware rikicin?

"Babban abin da ya kamata a yi shi ne a yi karatu ta-nasu. Idan dai suna so su samu nasara ko a yanzu ko kuma a zaben 2019 to ya kamata ne su hada kai."

Ya ce: "Ya kamata idan daya ya ja to sai daya ya saki. Ya kamata su yi hakuri da juna. Kuma kowane bangare a mutunta muradinsa."

Labarai masu alaka