'Ya kamata Buhari ya yi murabus domin kula da lafiyarsa'

Muhammadu Buhari
Image caption Shugaba Buhari ya tafi London ranar 7 ga watan Mayu

Wasu 'yan Najeriya na ta faman kiraye-kiraye da cewa shugaban kasar, Muhammad Buhari ya yi murabus.

A ranar Litinin din nan ne dai shugaban ke cika wata uku cif-cif da ficewa daga kasar domin jinya a London.

An dai ta ganin hotunan shugaba Buhari a baya-bayan tare da wasu gwamnoni da shugabannin jam'iyyar APC yayin wata ziyara da suka kai masa a London din.

Mutanen sun jaddada cewa shugaban yana murmurewa kuma ba da jimawa ba zai koma kasar.

To amma har kawo yanzu shugaba Buhari bai koma gida ba kuma rashin kasancewar tasa a kasar na ci gaba da janyo kace-nace har ma wasu na kiran da ya yi murabus.

Dr Kabiru Danladi Lawanti, malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria na daga cikin masu kiran shugaba Buharin da ya yi murabus.

Ya ce "A ra'ayina tunda har Buhari ya yi wata uku bai dawo ba ya kamata ya sauka domin kula da lafiyarsa."

Ya kara da cewa " Rashin lafiya da tsufa sannan ga matsalolin Najeriya da suka sha wa shugaban kai na bukatar ya je ya huta."

Dokar Najeriya dai ta nuna cewa idan har shugaban kasa ya kwashe kwana 90 ba ya kasar saboda rashin lafiya to ya kamata a ayyana shi da wanda ba zai iya ba a kuma rantsar da mataimakinsa.

Wasu kungiyoyin farar hula dai sun sha alwashin fara zaman dirshan a babban birnin kasar daga ranar Litinin.

Burinsu shi ne ko dai Buhari ya dawo kasar ko kuma majalisar kasa ta ayyana shi a matsayin maras koshin lafiyar da zai iya jagorantar kasar.