Rikici ya barke tsakanin al'ummar Hausawa a Lagos

'Yan sandan Najeriya
Image caption Tuni dai aka tura jami'an tsaro na 'yan sanda.

Rahotannin daga jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya na cewa wani rikici ya barke a tsakanin al'ummar Hausawa da ke a babbar kasuwa ta Alabarago.

Wasu rahotanni na cewa an garzaya da mutum takwas asibiti wadanda aka raunata.

Rikicin dai ya taso bayan kokarin da ake a sasanta tsakanin wasu sassa biyu da basa ga-maciji da juna a kan wanene shugaban kasuwar Alabarogo.

Tuni dai aka tura jami'an tsaro na 'yan sanda. Amma har yanzu 'yan sanda ba su ce komai ba kan batun.