'Yadda yarinya 'yar shekara 10 ta yi cikin shege a India'

An image depicting child abuse Hakkin mallakar hoto iStock

Wata yarinya 'yar shekara 10 da ta samu juna-biyu bayan an yi mata fyade, tana ci gaba da jan hankalin al'ummar kasar Indiya musamman bayan da kotu ta ki amincewa da bukatar zubar da cikin.

Wakiliyar BBC ta yi tattaki har zuwa arewacin birnin Chandigarh don ganawa da ita.

"Mun sha ganin yadda 'yan mata 'yan shekara 14 zuwa 15 sun yi ciki, amma wannnan ne karon farko da na taba ganin 'yar shekara 10 ta yi ciki", in ji Mahavir Singh wacce take aiki a hukumar ba da taimakon shari'a a birnin Chandigarh.

Mista Singh ta sa baki a al'amarin, wanda ya tayar wa da mutanen Chandigarh da sauran 'yan kasar hankali.

Yarinyar ta samu cikin ne bayan da ake zargin dan'uwanta da yi mata fyade a lokuta daban-daban.

Yanzu dai ana tsare da wanda ake zargin, don ya fuskanci shari'a.

Yarinyar da aka yi wa fyaden tana da fara'a. Tana da kunya kuma ba ta da magana sosai. Tana aji shida a makarantar firamare kuma tafi son darasin Turanci da lissafi. Tana son zane-zane kuma ta iya hakan sosai.

Sai dai a ranar 28 ga watan Yuli ne, kotun kolin Indiya ta ki amincewa da a bayar da damar zubar da cikin da take dauke da shi, saboda ya fara girma, ya kai kimanin mako 32.

Likita ya ba wa kotu shawarar cewa zubar da ciki zai iya jawo babbar barazana ga rayuwar yarinyar.

Sai dai umarnin kotun ya jefa 'yan uwan yarinyar cikin takaici.

'Ba ta da masaniya game da halin da take ciki'

Kotun Indiya ba su bayar da damar zubar da cikin ba, bayan da ya kai mako 20, har sai da likitoci suka tabbatar da cewa rayuwar yarinyar na iya shiga hadari.

Sai dai a shekarun baya-bayan nan, kotun ta samu kararraki da dama, yawanci ma na yaran da aka yi wa fyade, wadanda suke bukatar zubar da ciki bayan mako 20.

Hakan yana faruwa ne saboda sau da yawa, ba a gano cewa suna dauke da ciki da wuri don kasancewarsu yara ne kanana sosai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A Indiya ana yi wa yara 'yan kasa da shekara 16 fyade duk minti 155, 'yan kasa da shekara 10 kuma duk sa'a 13

A bangaren wannan yarinyar ma, a mako ukun da ya gabata ne aka gano yarinyar tana da ciki, a lokacin da ta fara korafin cewa mararta tana mata ciwo, daga nan ne mahaifiyarta ta kai ta wani asibiti.

Wani wanda ya san yarinyar ya ce: "Yarinyar ba ruwanta kuma ba ta son me ya faru da ita ba ma".

Har yanzu ba a sanar da yarinyar cewa tana dauke da juna-biyu ba, amma wadanda suke tare da ita sukan ce mata tana dauke da wani katon dutse ne a cikinta shi ya sa ya kumbura.

Ana ba ta abincin mai gina jiki irinsu kwai, da madara, da kifi, da kaza, da kayan marmari, shi ya sa take murna da irin kulawa ta musamman da ake ba ta.

Wani babban jami'i ya shaida wa BBC cewa, "ba ta gane hakikanin abin da yake faruwa ba, amma ina ganin yanzu ta dan fara fahimtar wani abu".

Iyayenta suna fafutukar yadda za su shawo kan matsalar.

Amma talakawa ne suna zaune a gida mai daki guda. Babanta ma'aikacin gwamnati ne mahaifiyarta kuma 'yar aiki ce a wani gidan masu hali.

Wata 'yar sanda Pratibha Kumari, wacce take binciken al'amarin ta bayyana su a matsayin "zuri'a ta gari, wadanda suke da saukin kai, shi ya sa ba su gano abin da wannan mutumin yake yi wa 'yar su ba."

Ta ce, "duk sanda mahaifiyarta take mun magana tana kuka. Babanta ya ce yana jin tamkar an kashe masa 'yarsa ne".

Hakkin mallakar hoto AFP

Abin da ya sa al'amarin ya yi muni shi ne, tun da ake samun labarin fyade da ciki ba a taba samun mummuna kamar wannnan ba.

Tunda wanda ake zargi da yin fyaden dan'uwar mahaifiyarta ne, wasu suna tambaya indai ta san da hakan, to "me ya sa ba ta san 'yarta tana da ciki ba, har tsawon wata bakwai?

Wannan babban tashin hankali ne ga 'yan uwanta, kuma mahaifinta yana cikin bakin-ciki da takaici.

"Ina so a yi masa hukunci mai tsanani. ko ma a yanke masa hukuncin kisa ko a yi masa daurin rai-da rai. Saboda ya aikata laifi. Amma bai taba ba mu hakuri ba," in ji mahaifiyar yarinyar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu fafautuka sun ce kashi 50 cikin 100 na wadanda suke yin fyade makusantan yaran ne ko wadanda aka yarda da su

Kowacce shekara, mata 45,000 suke mutuwa wajen haihuwa a Indiya, likitoci sun ce hadarin zai fi ta'azzara ga yarinyar karama 'yar shekara 10 .

Tun da iyayen yarinyar sun ce ba abin da za su yi da jaririn da za ta haifa, kwamitin kula da kananan yara ya ce zai kula da shi.

'Yar shekara 10 za ta iya haihuwa? Muna addu'a kada wani abu mara dadi ya same ta".

Labarai masu alaka

Karin bayani