Nigeria: Doguwa ne shugaban APC a Kano – Bolaji Abdullahi

Kwankwaso da Ganduje Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jam'iyyar ta rabu gida biyu ne a jihar wato bangaren Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso

Uwar jam'iyyar APC ta ce har yanzu Alhaji Umar Haruna Doguwa ne, shugabanta a jihar Kano, sabanin wasu rahotanni da ke cewa an tube shi.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar ta ce kwamitin gudanarwar APC na kasa bai taba cim ma wata shawara game da tube Haruna Doguwa ba.

A ranar Asabar da ta gabata ce, jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta gudanar da wani babban taro don cike guraben wasu kusoshinta, sai dai bangaren Umar Haruna Doguwa ya kaurace.

Yayin taron wanda aka gudanar karkashin jagorancin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje an tabbatar da zaben Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar a Kano.

Doguwa yana bangaren tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne, yayin da Alhaji Abdullahi Abbas yake samun goyon bayan Gwamna Ganduje.

Uwar jam'iyyar APC ta kasa ta ce tana sane da wasu batutuwa a cikin jam'iyyar APC reshen Kano, kuma tana ci gaba da kokari don kawo karshen matsalar.

A cewarta, bisa la'akari da haka, za a ci gaba da tafiya a kan matsayar da ake kai, ya zuwa lokacin da za a kammala kokarin sasantawa.

Labarai masu alaka