Nigeria 'Muna bayan Buhari har sai ya shekara takwas'

Mawaki Charly Boy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Litinin ne wani mawaki mai suna, Charly Boy, ya shirya zanga-zanga a Abuja, inda aka bukaci shugaban ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka

'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan kiraye-kirayen Shugaba Muhammadu Buhari ya koma gida ko kuma ya yi murabus saboda ya cika wata uku yana jinya a kasar Birtaniya, kamar yadda wasu 'yan kasar suka bayyana.

A ranar Litinin ne wani mawaki mai suna, Charly Boy, ya shirya wata zanga-zanga a Abuja, inda aka bukaci shugaban ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka.

A muhawarar da aka tafka a shafukan sada zumunta na BBC Hausa Facebook da kuma Twitter mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu.

Ga kadan daga cikinsu:

Saifullahi Idris ya mayar da martani ne ga masu zangar-zangar inda ya ce: "Wahala ce ba ta ishe su ba, babu ranar yin murabus din Shugaba Buhari."

"Wadannan 'yan tsirarun ba su isa su sa Buhari ya yi murabus ba," in ji Muhammad Sani Aliyu Camry.

Mahmud Hassan Abu Aisha, ya jaddada goyon bayansa ne ga shugaban: "Muna tare da Baba Buhari har sai ya gama shekaru takwas Insha Allah," in ji shi.


Hakazalika shi ma Sani Ashahura Maigoro, "Ni dai ina tare da Shugaba Muhammadu Buhari dari bisa dari. Kuma wallahi muna nan, muna yi ma sa addu'a. Duk masu yi mai zagon kasa Allah Ya karya su baki daya," in ji shi.

Amma ra'ayin Naseer Inuwa Mijinyawa Tabbas ya sha bamban don cewa ya yi: "Tabbas ya kamata Buhari ya yi murabus saboda ya je ya nemi lafiya, don hakan ya fi masa kyau."

Har ila yau akwai masu ganin kamata ya yi 'yan kasar su koma wa Allah.

"Zanga-zanga da aka yi a Abuja kan Buhari ya yi murabus, ba shi ne mafita ba. Yi wa shugaban addu'a shi ne mafita",in ji Muhammad Garin Rijiya.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"

5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"

28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba

3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu

7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya

25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya

11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a Landan

23 ga watan Yuli - Ya gana da wasu gwamnoni

26 ga watan Yuli - Ya sake ganawa da wasu karin gwamnoni

Karanta karin labarai kan Buhari:

Labarai masu alaka