Masallacin da mace ke limanci a Berlin na tayar da kura

Limamiya Seyran Ates
Image caption Masallacin dai na maraba da kowa da kowa

A Berlin, an bude wani sabon masallaci da ke maraba da cudanyar maza da mata domin yin sallah tare a lokaci guda.

Masallacin kuma na bayan wani cocin da aka gina ne tun a karni na goma sha tara.

Mata ne dai ke limanci a lokacin yin Sallar kuma masallacin na maraba da matan da ba sa yin lullubi.

Har wa yau, wannan masallacin na maraba da 'yan luwadi da 'yan madigo da kuma mata-maza.

Shugabanni masallacin dai na cewa sun dauki matakin ne da zimmar tafiya tare da kowa cikin addinin da suka ce na Islama ne.

Wata mai fafutukar kare hakkin bil'adama mai suna Seyran Ates ce ta bude masallacin mai lakabin Ibn Rushd-Goethe Mosque.

Tuni dai wasu musulmi suka fara sukar wannan tsarin da suke bayyana shi da makirci.

Image caption Fuskar cocin da masallacin Seyran Ates ke ciki
Image caption Mata da maza a sahun sallah a masallacin Seyran Ates
Image caption Wata mace na koyawa namiji karatun Qur'ani