Cin hanci: Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya

Magoya bayan Shugaba Zuma na murna a birnin Cape Town Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan Shugaba Zuma na murna a birnin Cape Town

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya sha da kyar a kuri'a ta baya-bayan nan da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada domin tsige shi daga kan mulki.

'Yan adawa sun yi fatan cewa kada kuri'ar a sirri zai sa 'yan majalisar jam'iyyarsa ta ANC su juya masa baya.

Sai dai a kuri'ar, wacce aka shirya saboda zargin cin hanci da ake wa shugaban, ya samu rinjaye da 198 yayin da 'yan hamayya suka samu 177.

'Yan majalisar jam'iyyarsa ta ANC sun barke da murna lokacin da aka sanar da sakamakon kuri'ar.

Ana bukatar 'yan jam'iyyar ANC akalla 50 daga cikin 249 su juya wa shugaban baya kafin a iya tsige shi.

Sai dai sakamakon ya nuna cewa akalla 'yan ANC 26 ne suka juya wa shugaban baya, yayin da tara suka kauracewa kuri'ar.

Tun da farko shugabannin adawar sun yi gargadin cewa Afirka ta Kudu za ta kama hanyar "mutuwa" idan har Shugaba Zuma ya tsallake kuri'ar.