Boko Haram: 'An kashe masunta 31 a Baga'

Ba wannan ne karo na farko da mayakanm suka taba kai hari kan masunta a yankin tafkin Chadi ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba wannan ne karo na farko da mayakanm suka taba kai hari kan masunta a yankin tafkin Chadi ba

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe wasu masunta 31 a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno a arewacin Najeriya.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce wannan hari na nuna cewa har yanzu mayakan kungiyar na kai hare-hare masu muni da kashe mutane a yankin tafkin tekun Chadi.

Sai dai gwamna Shettima ya ce har yanzu jami'an tsaro ba su tabatar da rahoton harin ba.

Ya ce shi ma ya samu kiran waya ne daga wasu da ke yankin, wadanda suka shaida lamarin, suka kuma tabbatar masa da hakan.

Amma ya nuna matukar damuwarsa kan abin da ya kira ci-gaba da ayyukan 'rashin tausayi' da mayakan ke yi a arewa maso gabashin kasar.

Gwamna Shettima ya yaba wa rundunar sojin kasar kan kokarin da take na dawo da zama lafiya a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Najkeriya, NAN, ya ruwaito cewa, ko a ranar 5 da 6 ga watan Agustan nan ma, mayakan Boko Haram sun kai wasu hare-hare guda biyu kan masunta a wasu garuruwa na Baga.

NAN ya ce, wani dan kato da gora ya bayyana cewa an kashe mutum 14 a harin Duguri da kuma mutum 17 a harin Dabar-Wanzam.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnan Borno ya yaba wa rundunar sojin Najeriya don kokarinta na kawo zaman lafiya

An kai wadannan hare-hare ne mako hudu bayan da masuntan suka dawo da ci gaba da sana'arsu ta kamun kifi a yankin.

Dauke haramcin kamun kifi da rudunar sojin ta yi a baya-bayan nan dai ya jawo hankalin dubban masunta inda suka koma don ci gaba da sana'ar tasu.

A baya rundunar sojin ta haramta kamun kifin ne saboda Boko Haram ta ce tana samun kudin da take sayen makamai ne daga aikin kamun kifi a yankin.

Labarai masu alaka