Gwamnonin arewa za su ba Borno tallafin N360m

Cikin wuraren da gwamnonin suka kai ziyara a Bornon har da sansanin 'yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cikin wuraren da gwamnonin suka kai ziyara a Bornon har da sansanin 'yan gudun hijira

Gwamnonin jihohin arewa sun kai wata ziyara zuwa jihar Borno domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar, kan hare-haren 'yan ta-da-kayar-baya na baya-bayan nan.

Gwamnonin sun yi alkawarin bai wa jihar Borno tallafin Naira miliyan 360, inda kowacce daga jiha 19 a yankin (ban da Borno) za ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 20.

Yayin wannan ziyara da gwamnonin suka kai Maiduguri ranar Talata, cikin ayarin akwai gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, da Nasir El-Rufa'i na Kaduna sai kuma Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da na Adamawa Jibrilla Bindow.

Ayarin gwamnonin ya ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira domin ganin halin da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu ke ciki.

A baya-bayan nan dai, kungiyar Boko Haram ta zafafa kai hare-hare, inda a karshen watan jiya ta far wa wani ayarin ma'aikatan binciken man fetur, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 40 tare da sace wasu.

Haka zalika, a daidai lokacin da gwamnonin ke wannan ziyarar, rahotanni na ci gaba da fitowa kan wani hari da kungiyar ta kai inda ta hallaka masunta sama da 30 a wani tsibiri da ke yankin tafkin Chadi.

Labarai masu alaka