Wa zai lashe zaben Kenya?

Ana cigaba da kirga kuri'un zaben na kasar Kenya, inda wasu masu kada kuri'a shafe kwana guda kan layi suna jiran yin zabe.

Queue outside polling station in Nairobi city centre Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption People began queuing early in the morning and even overnight to cast their votes

An bar wasu rumfunan zaben bude har bayan karfe biyar na yamma, watau biyu kenan agogon GMT, lokacin da wa'adin kada kuri'a ya cika, sanadiyyar matsalar da aka samu na ruwa kamar da bakin kwarya da wasu 'yan matsaloli kadan da suka sa zaben ya dan ja.

Shugaba Uhuru Kenyatta na fatan sake hawa mulki a karo na biyu, amma yana fuskantar barazana daga abokin hamayyarsa, Raila Odinga.

Yawancin al'ummar Kenya na fargbar barkewar rikici bayan zaben, makamancin wanda aka samu a zaben shekarar 2007, inda sama da mutane 1200 suka rasa rayukansu, yayin da mutane dubu dari shida suka rasa muhallansu.

An riga an samu sakamakon wasu mazabun, amma akwai yiwuwar a yi dakon kwana da kwanaki kafin cikakken sakamakon zaben ya fito.

Dan takaran shugaban kasar na bukatar kashi 50 cikin dari na kuri'un, da kuma akalla kashi 25 cikin dari na 24 daga cikin lardunan 47 da Kenya ke da su.

Idan babu wanda ya samu adadin kuri'un da ake bukata , sai a bukaci zaben zagaye na biyu, tsakanin 'yan takarar biyu mafiya yawan kuri'u.

Shi dai shugaba Uhuru Kenyatta dake kan mulki ya yi alkawarin mutunta zabin da jama'a suka yi.

Baya ga zaben shugaban kasar akwai kuma takara mai zafi a zaben 'yan majalisar dokoki da kuma na shugabannin kananan hukumomi.

Fatan al'umar Kenya shi ne a gudanar da sahihin zabe, kuma karbabbe, wanda zai tabatar da dorewar kasar ta fuskar siyasa da kuma tattalin arzikinta, a yanayin da ake ciki mai matukar muhimmanci.