Kuri'a: Yan jam'iyar ANC sun yi zurfin tunani — Masani

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu
Image caption Wannan ne dai karo na takwas da shugaba Zuma ke tsallake kuri'ar yanke kauna da 'yan Majalisar dokokin kasar ke yi a kan sa

Masana na ci gaba da tsokaci dangane da sha da kyar da Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi a kuri'ar da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada don neman tsige shi daga kan mulki.

Wannan ne dai karo na takwas da shugaba Zuma ke tsallake kuri'ar yanke kauna da 'yan Majalisar dokokin kasar ke yi a kan sa.

Tun da farko dai 'yan adawa sun yi fatan cewa, kada kuri'ar da aka yi a asirce zai sa 'yan majalisar daga jam'iyyar sa ta ANC su juya masa baya.

Sai dai a kuri'ar, wacce aka shirya saboda zargin cin hanci da ake wa shugaban, ya samu rinjaye da 198 yayin da 'yan hamayya suka samu 177.

Dr. Bala Muhammad, malami a Jami'ar Bayero ta Kano da ke Nigeria ya ce 'yan jam'iyar ANC da ke majalisar ne za su gwammace kida da karatu muddin suka sa aka tsige shugaba Zuma.

""Idan suka sa aka cire Zuma mecece ribarsu?, kuma ina aka dosa, idan suka cire shi ba su san abin da zai biyo baya ba.'' In ji shi.

Ya kara da cewa da alamu 'yan majalisar sun yi duban hankali ne daga bisani, suka ga cewa idan suka sake aka cire Zuma sune za su fi tafka asara.

''Watakila sun yadda da dukkan abinda ake fada na laifin Jacob Zuma, amma kuma suna duba cewa idan aka cire shi aka samu hargitsi a jam'iyar za su samu koma baya'', in ji masanin.

Tun da farko shugabannin adawar sun yi gargadin cewa Afirka ta Kudu za ta kama hanyar "mutuwa" idan har Shugaba Zuma ya tsallake kuri'ar.

Labarai masu alaka