An yi girgizar kasa sau 2 cikin sa'o'i 24 a kasar China

Kasar China
Image caption An rika jin karfin girgizar kasar a yankin Xian, da ke da nisan kilomita dari daga inda ta faru

An samu girgizar kasa har sau biyu a kasar China cikin kasa da kwana guda abinda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane 7 da jikkatar wasu sama da 60 a larduna Xinjian da Sichuan.

Ta baya-bayan nan ta faru ne a kusa da kan iyakar kasar ta China da kasar Kazakhstan, a lardin in Xinjian.

Ba dai a samu rahoton barnar da ta yi ba.

Amma kuma ta farkon wadda ta afka wa wani yanki mai tsaunuka da ke kusu maso yammacin kasar ta hallaka akalla mutane 7, tare da jikkata gwammai.

Ta kuma faru ne a kusa da wani sanannen wurin zuwan baki 'yan yawon bude ido da ke lardin Sichuan da ake kira-- gandun dajin Jiuz-haigou .

Kana an samu zafrewar laka, wacce ta rutsa da 'yan yawon bude ido kusan dari, tare da lalata dubban gidaje.

Inda girgizar kasar ta fi muni yanki ne da ke da karancin jama'a da galibi 'yan kabilar Tibet ne ke zaune.

Wasu rahotanni sun ce adadin wadanda suka mutun ka iya karuwa.

Lardin Sichuan yanki ne da ke fuskantar barazanar yawan afkuwar girgizar kasa.

Mutane fiye da 70,000 suka mutu a girgizar kasar a shekara ta 2008.

Wasu hotuna sun nuna lalatattun gine-gine, da suka hada da otal a garin Jiuzhaigou, inda ke da sanannen wurin adana kayan tarihi na duniya da Majalisar Dinkin Duniya da ayyana.

Wata mai gidan abinci a garin ta ce karfin girgizar kasar ya fi na shekara ta 2008, duk da cewa babu wasu bayanai da suka nuna cewa adadin wadanda suka mutu zai kai ko kusa da wanda ya faru a wancan lokacin.

Tang Sesheng ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, mutane da dama sun tsere daga gidajensu a garin na Jiuzhaigou.

"Mutane ba su iya saukar komai ba kama daga kudi ko tufafi ba-mun kawai ruga da gudu ne,'' ta ce.