'Yan Kenya na cike da fargaba kan sakamakon zabe

Raila Odinga Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Odinga sya ce an tafka magudi a zaben

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a zaben Kenya, Mista Raila Odinga, ya ce an yi wa kwamfyutocin hukumar zaben kasar kutse don jirkita sakamakon kuri'un da aka kada.

Ya yi watsi da sakamakon farko-farko na zaben ranar Talata, da ke nuna cewa Shugaban kasar Uhuru Kenyatta yana kan gaba da babbar rata.

Shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati, ya ce yana da kwarin gwiwa a kan ingancin na'urorinsu amma dai za a gudanar da bincike a kan wannan ikirari.

Mutane da dama na fargaba game da sake aukuwar tarzoma bayan zaben kasar mai cike da takaddama shekara goma da ta wuce, don haka ake ta kiraye-kirayen kwantar da hankula.

'Yan Kenya fiye da 1,100 ne suka mutu, aka kuma raba wasu kimanin 600,000 da gidajensu bayan zaben shekara ta 2007.

Jami'an zabe sun ce bayan karbar sakamakon kuri'un da aka kada kashi 91%, Shugaba Kenyatta ne yake kan gaba da kimanin kashi 54.5%, a kan kashi 44.6% na abokin fafatawarsa Raila Odinga.

Sakamakon na nuni da cewa ga alama Mista Kenyatta ya kama hanyar samun nasara a zagayen farko.

Don kauce wa zuwa zagaye na biyu, daya daga cikin 'yan takarar yana bukatar samun kashi 50% da karin kuri'a daya da kuma akalla kashi 25% na kuri'un da kada a 24 cikin yanki 47 na Kenya.

'Yan takara guda takwas ne duka-duka suka tsaya, sai dai baya ga Mista Kenyatta da Raila Odinga, babu wani da ya samu ko rabin kashi 1% na kuri'u.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai, Mista Odinga, wanda ke jagorantar wani kawance mai taken National Super Alliance (Nasa), ya ce kamata ya yi magoya bayansa su kwantar da hankula.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan kwantar da tarzoma suna ta yawo a titin Kisumu da ke Kudancin Kenya

Sai dai a babbar tungar 'yan adawa ta Kisumu, a yammacin Kenya, wani mai aiko wa BBC rahotanni ya ga gungun daruruwan magoya bayan Mista Odinga na gudanar da zanga-zanga inda suke kururuwar cewa: "Ba Raila, ba zaman lafiya".

Daga nan, sai 'yan sanda suka tarwatsa su ta hanyar harba hayaki mai sa hawaye.

Da yake jawabi a Nairobi babban birnin kasar, Ministan tsaron cikin gida Fred Matiang'i ya bukaci 'yan Kenya su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba, ya ce bai samu wani rahoton tashin hankali ba, bayan kammala zaben.

Ya kuma ce ana iya katse sadarwar shafukan sada zumunta matukar suka zama "barazana ga tsaron kasa".

Hakkin mallakar hoto Ronald Grant

Labarai masu alaka