Jirgin yakin Nigeria ya 'kashe 'yan Boko Haram da dama'

Nigerian Jet Hakkin mallakar hoto NAF
Image caption Rundunar sojin saman ta ce ta shafe tsawon kwana daya tana tantance bayanai kafin ta kai hari a kan maboyar

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce wani jirgin yakinta da ke cikin shirin Zaman Lafiya Dole ya kai hare-hare kan wata maboyar wasu 'yan Boko Haram, inda ya kashe da dama a cikinsu.

Wata sanarwa da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Air Commodore Olatokunbo Adesanya ya fitar, ta ce jirgin yakin ya yi luguden wuta a kan maboyar, wadda ke yankin Parisu a dajin Sambisa, a ranar Talata.

A cewarta, harin ya biyo bayan wani gungun 'yan Boko Haram da aka hango suna taruwa a karkashin wata bishiya kusa da wani gini, inda aka yi amfani da rassan bishiya wajen rufe maboyar.

Ta ce jirgin yakin ya fara yin luguden wuta a kan maboyar wadda bayanai suka nuna cewa mayakan Boko Haram ne, kafin kuma ya kai hari a kan wani gini shi ma da yake kusa.

Sanarwar ta ce daga bayanan da dakarunta suka tattara, akwai 'yan Boko Haram da yawa da ke amfani da wajen suna boyewa.

Ta ce a harin farko da na biyu, ginin ya yi raga-raga, yayin da hari na uku kuma ya tarwatsa yankin.

Rundunar ta ce baya ga 'yan Boko Haram da suka mutu a harin, an kuma ga wasu kalilan suna kwashe wadanda suka mutu ko suka ji raunuka.

A cikin makon jiya ne, manyan hafsoshin sojan kasar suka koma Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas, sakamakon zafafa hare-hare da kungiyar Boko Haram ta yi.

A baya-bayan nan ma, mayakan kungiyar sun kashe masunta 31 a wani tsibiri da ke yankin tafkin Chadi.

Labarai masu alaka