Nigeria: Wane irin tasiri Lungu-Kalkal zai yi a Kano?

Aikin magudanar ruwa a birnin Kano Nigeria
Image caption Jama'ar birnin Kano da dama na fama da matsalar ambaliyar ruwa saboda rashin lambatu a lunguna

Mazauna birnin Kano da ke arewacin Najeriya na fama da matsalolin cunkoson jama`a da cushewar gidaje da magudanan ruwa, lamarin da ke haddasa ambaliyar ruwa da barkewar cututtuka.

Shekaru aru aru da suka shude birnin Kano, wato tsohon zama da aka fi sani da cikin badala ya kasance abin alfahari da tunkaho ga 'yan gari, ga baki kuma wurin da kowa ke son ziyarta.

Sai da a baya-bayan nan fasalin birnin da rayuwar mazaunansa na sauyawa sakamakon conkuson jama'a da cushewar gidaje, lamarin da ya haddasa karancin hanyoyin zirga-zirga da toshewar magudanan ruwa.

Kuma a irin wananan yanayi na damina, masu karamin karfi su kan fada cikin halin ha'ula'in ambaliyar ruwa.

''Idan aka yi ruwa za mu yi sa'o'i biyar ba mu fito daga cikin gidajenmu ba saboda kududdufi bakwai ne ke biyowa ta kan hanyar kwatamin nan,'' inji wani mazauni tsohon garin.

Wani kuma ya kara da cewa: ''ruwa ne yake cinye mu har daki, ya kashe mutum, ya tafi da mutum, ya karya mutum, wannan kwata ta dame mu ta addabe mu!''.

Amma gwamnatin jihar ta kaddamar da wani shiri mai suna Lungu-kalkal da nufin magance matsalar, inda ake kashe dubban miliyoyin naira.

Image caption Galibin hanyoyin cikin birnin Kanon a tsuke suke saboda cunkoson gidaje

Wakilin BBC a yankin da ya leka daya daga cikin ungwannin da ake gudanar da aikin gina magudanan ruwan a cikin birnin ya ga yadda ma'aikata da injiniyoyi suka dukufa suna aiki.

Injijniya Sume Yakubu daya daga cikin injiniyoyin ya ce babbar magudanar ruwan da suke ginawa tana da fadin kusan mita daya da digo daya, da kuma zurfin mita daya da digo daya.

Hukumomin jihar sun ce bayan kawata muhalli aikin zai taimaka wajen inganta lafiyar al'umma.

Hon Shehu Haruna Lambu babban jami'in gwamnatin jihar Kanon ne da ya bayyana cewa bayan ga cizon sauro da yaduwarsa, akwai matsala ta wari da gurbacewar iska da ke haifar da annobar kwalara.

Ya kuma ce: ''shi yasa mai girma gwamna ya ce a je cikin birnin lungu da sako a gina madatsun ruwan a kuma kawata su da fitilu''.

Sai dai kuma yayin da gwamnatin jihar ke wannan aiki, wasu na sukar lamirinta bisa la'akari da makudan kudaden da aikin yake ci.

Labarai masu alaka