Masu fasa-kwauri sun jefa mutum 50 cikin teku — IOM

Bakin tekun kasar Yemen Hakkin mallakar hoto IOM
Image caption Jami'an hukumar IOM ne suka gano wadanda suka tsira da rayukansu a bakin tekun Shabwa, a kasar Yemen

Hukumar lura da masu kaura ta Majalisar Dinkin Duniya I.O.M, ta ce masu fasa-kwaurin mutane sun tunkuda 'yan ci-ranin kasashen Somalia da Habasha kusan 50 a cikin tekun kasar Yemen da gangan.

Hukumar ta I.O.M. din ta ce a ranar Laraba ne aka tilastawa 'yan ci-rani fiye da 120 fadawa cikin tekun.

Akalla 29 ne suka mutu a cikin su, bayan da ma'aikatan agaji suka gano gawawwakinsu a bakin tekun na Yemen.

An kuma binne su a wasu ramuka marasa zurfi da ake kyautata zaton wadanda suka tsira ne suka yi hakan.

Suna cikin mutane 120 da masu fasa kwaurin suka durmuyar daga cikin jirgin zuwa cikin tekun saboda tsoron kada jami'an tsaro su kama su.

Hukumar ta I.O.M ta kuma gano mutane 27 da suka tsira a bakin tekun a yayinda suke sintiri.

Har yanzu in ji hukumar ba a gano inda sauran 22 suke ba, yayinda sauran suka kara gaba, in ji hukumar.

Akasarin wadanda ke cikin jirgin ruwan matasa ne da ke fatan isa kasashen yankin Gulf ta cikin kasar Yemen.

Labarai masu alaka