An bai wa ma'aikata hutu saboda tsananin zafi a Iraki

Wani dan Iraki na yanka kankarar sayarwa a Baghdad ran 6 ga watan Yulin 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu sayar da kankara na matukar ciniki cikin wanan yanayi na tsananin zafi

Firai ministan Iraki Haider al-Abadi, ya bai wa dukkan ma'aikatan gwamnati umarni ka da su je aiki ranar Alhamis, saboda tsananin zafin da ke yi, irin wanda ba a cika yi ba.

Masu hasashen yanayi suna tsammanin yanayin zafi a ranar Alhamis a babban birnin kasar Baghdad, zai kai maki 50 a matakin salshiyas.

Baya ga birnin Baghdad, ana kuma tsammanin za a yi tsananin zafi a biranen Basra da Mosul.

Tsananin zafin zai iya jawo rashin wutar lantarki, wanda hakan zai sanya mutane cikin tsanani, da zai tsayar da al'amuran kasuwanci da sana'o'i.

A makonni baya-bayan nan dai an yi ta tsananin zafi a yankin Gabasa Ta Tsakiya, har hakan ya dan shafi wasu sassa na Turai.

Masana kimiyya sun yi gargadi cewa yanayin tsananin zafin zai iya jawo mutuwar mutum 52,000 duk shekara a Turai nan da shekarar 2100, idan har ba a yi wata hobbasa don dakatar da

Labarai masu alaka

Karin bayani