Kun san tsohuwar da ta kammala digiri a shekara 91?

Kimlan Jinakul Hakkin mallakar hoto Panumas Sanguanwong/BBC Thai
Image caption Kimlan na daya daga cikin dubban wadanda suka kammala digirinsu a bana

Wata tsohuwa 'yar kasar Thailand mai shekara 91 ta ce, "Gemu ba ya hana neman ilimi", inda ta kammala digirinta bayan ta shafe shekara goma tana yi, a tattaunawar da suka yi da wakilin BBC.

Kimlan Jinakul, tana da burin ta yi karatu a jami'a, sai dai ba ta samu wannan damar ba a lokacin da take da kuruciya.

Daga baya ne lokacin da ta ga yawancin 'ya'yanta sun kammala karatu a jami'ar, sai ta yanke shawarar fara karatun nata, kuma a ranar Larabar nan ne ta kammala digiri.

Kimlan 'yar asalin lardin Lampang ce da ke arewacin Thailand. Daliba ce mai kwazo kuma ta yi karatu a daya daga cikin fitattun makarantun lardin.

Sai dai karatu a jami'a a wannan lokacin ba abu ne mai sauki ba, daga baya kuma sai suka koma Bangkok, sai ta yi aure saboda haka sai ta daina tunanin cika burinta na ci gaba da karatu.

"Ko da yaushe ina burin naga 'yayana sun yi karatu. Saboda haka ne nake ba su kwarin gwiwa da goyon baya a lokacin da suke karatu a jami'a."

Hakkin mallakar hoto Panumas Sanguanwong/BBC Thai
Image caption Yawancin iyalan Kimlan sun halarci murnar kammala digirinta

'Yayanta hudu sun kammala digiri na biyu, dayar kuma tana karatun digiri na uku a Amurka.

Karatun da 'yayanta suka yi ne ya ja ra'ayinta ita ma ta yi nata.

Rayuwar farin ciki

A lokacin da daya daga cikin 'ya'yanta wacce take aikin asibiti yanzu, ta yi karatu a Jami'ar Sukhothai Thammathirat, sai Kimlian ta yanke shawarar fara nata karatun ita ma.

Lokacin da ta samu gurbin karatunta na farko tana da shekara 72, sai dai a lokacin tana cikin damuwa sakamakon mutuwar 'yarta wacce suke karatu tare a lokacin. Saboda haka ta ajiye karatun na dan wasu shekaru.

A lokacin da ta kai shekara 85 ne ta sake samun gurbin karatu karo na biyu a fannin kimiyya, inda ta ce karatun zai koyar da ita yadda za ta zauna lafiya ta yi rayuwa mai dadi.

Ta shada wa BBC cewa, "Bayan da na fara farfadowa daga damuwar rashin da na yi, na mayar da hankali don na kammala karatun.

Hakkin mallakar hoto JUASIRIPUKDEE'S FAMILY
Image caption Kimlan ta shafe shekara 10 kafin ta kammala digirinta

"Ba a girma da karatu. Ko da yaushe zuciyata na son karatu", in ji Kimlan.

Ta kara da cewa, "Duniyar ba za ta kare ba, ko da yaushe ana kara samun sababbin matsalolin da za mu iya magance su. Idan ba a samun sabbabin nazarin kimiyya ba to za a daina samun ci gaba a duniya.

Hanyoyin da na bi nayi nasara

Da aka tambayeta game da sirrin nasararta, sai ta ce, abin sa kai ne da kuma burin da nake da shi tun da dadewa.

"Lokacin da na sa a raina ina so na kammala karanta babi daya, zan yi iya kokarina na gama. Sai na ja layi a kan kalmomi masu muhimmanci wadanda nake son na haddace. Wannan ne ya taimaka min a lokacin da nake karatuna.

"Ina yin farin-ciki idan na yi nasara, kuma ina jin bakin-ciki idan na fadi. Saboda haka idan na fadi ina sake yin jarabawar har sai na ci", sai ta yi dariya.

Da aka tambayeta, wanne shirin take sake yi bayan kammala digirinta?

Sai ta ce, "Na san ma ba wanda zai ba ni aiki idan ina nema," ta fada da raha.

"Kawai zan ci gaba da kula da jikokina," in ji ta.

Labarai masu alaka

Karin bayani