Za a ci kyautar dala 2000 a Gasar Hikayata ta 2017

Hikayata
Image caption Aisha Sabitu ce gwarzuwar gasar Hikayata a karon farko a bara

Shin ina mata iyayen giji? Sashen Hausa na BBC ya sake bude gasar rubuta ƙagaggun labarai ta mata zalla a karo na biyu.

Gasar Hikayata, wani kokari ne na bai wa mata damar fito irin basirar da Allah ya hore musu wajen rubutu da kirkirar labari.

Ga masu sha'awar shiga gasar sai su rubuta ƙagaggen labari wanda bai fi tsawon kalma 1,000 zuwa 1,500 ba, daga ranar Talata, 15 ga watan Agusta, 2017.

Ana iya aiko da rubutun ta hanyar imel na Labari.bbchausa@bbc.co.uk har zuwa ranar Lahadi 10 ga watan Satumba da za a rufe gasar.

A ranar 1 ga watan Agustan 2016 ne Sashen Hausa na BBC ya fara karbar kagaggun labarai a wannan gasa ta mata zalla karon farko a tarihi.

Za a iya karanta ka'idojin shiga gasar a nan.

Image caption Gasar ta mata ce zalla
Image caption Hikayata gasa ce ta rubutu don mata kawai

Wannan gasa tana da burin taimakawa wajen bunkasa rubutu a tsakanin mata da rage gibin da ke tsakaninsu da maza, wanda rashin daidaito ta fuskar samar da ilimi ya haifar.

A karon farko na gasar Hikayata, Aisha Muhammad Sabitu ce ta zama gwarzuwa, inda aka ba ta lambar yabo da kuma $500.

Aisha, wadda ta fito daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labari mai suna "Sansanin 'Yan Gudun Hijira".

Sai kuma, Amina Hassan Abdulsalam ta zo ta biyu, da labarinta mai suna "Sai Yaushe?", yayin da Amina Gambo ta zo ta uku da labarin "In Da Rai".

Image caption Karo na biyu kenan da BBC Hausa take bude gasar Hikayata saboda mata zalla

Labarai masu alaka