'Yakin Amurka da Koriya zai iya kawo karshen duniya'

Kim Jong-un and Donald Trump (composite image) Hakkin mallakar hoto Getty Images and Reuters
Image caption Shugaba Trump ya ce "zan mayar wa Koriya martani da duniya ba ta taba ganin irinsa ba"

Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin mayar da martani mai zafi ga duk wata barazana da kasar Koriya ta Arewa take yi wa kasarsa.

Ya ce martanin zai zama "wanda ba a taba ganin irin shi ba a tarihin duniya".

A halin da ake ciki yanzu, Koriya ta Arewa na yin barazanar kaddamar da harin makami mai linzami a yankin tsibirin Guam da ke Amurka, inda mutum 163,000 ke zaune.

Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton cewa, Koriya ta Arewa na kokarin samun nasara wajen rage rikicin makami mai linzamin da zai iya shafar wasu kasashe, wani abin da Amurka da kawayenta na Asiya suka dade suna fargabar faruwarsa.

Ko wannan wata alama ce ta shiga filin daga don kece rainin?

Masu sharhi sun ce kar ku tayar da hankali kan wannan batu tukunna. Ga dalilan da suka ba da:

1. Ba wanda yake son yaki

Wannan na daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ya kamata musa a ranmu. Ba wanda yake son yakin don ba zai taimakawa kowa ba.

Babban burin gwamnatin Koriya ta Arewa shi ne samun kwanciyar hankali, kuma yaki da Amurka ka iya jawo tsananin tashin hankali.

Wakilin BBC kan al'amuran tsaro ya yi bayanin cewa, duk wani harin Koriya ta Arewa a kan Amurka ko kawayenta a yanzu ka iya jawo gagarumin yakin da zai shafi duniya, kuma ya dace mu sa a ranmu cewa gwamntin Kim Jong-un ba ta kunar bakin-wake ba ce.

A takaice, wannan ne ya sa Koriya ta Arewa take iya kokarinta ta zama tana da karfin makami mai linzami.

Samun wannan damar dalilai ne na yiyuwar kare gwamnatin ta hanyar karin kudin shiga.

Kim Jong-un ba ya so ya zama marigayi Muammar Gaddafi na Libya, ko kuma marigayi Saddam Hussein na Iraqi.

Andrei Lankov na Jami'ar Kookmin da ke Seoul, ya shaida wa jaridar Guardian cewa, "akwai yiyuwar samun tashin hankali", amma Koriya ta Arewa ba ta da ra'ayin bin hanyar diflomasiyya a wannan lokacin.

"Da farko suna son su samu damar cire birnin Chicago daga taswirar duniya, sannan kuma sai su nuna ra'ayinsu a kan mafita ta bin hanyar diflomasiyya", in ji Mista Lnkov.

Amurka ta san cewa harin da za ta kai wa Koriya ta Arewa zai tilasta wa Koriyar mayar da martani kan kawayen Amurka, wato kasashen Koriya ta Kudu da kuma Japan.

Wanda hakan zai jawo asarar rayuka da suka hada da dubbban 'yan Amurka, da sojoji da kuma fararen hula.

Dadin-dadawa, Washington ba ta bukatar duk wata kasadar kaddamar da harin makami mai linzamin da za a kai wa Amurka.

2. Abin da kuke gani a baki ne kawai, amma ba a filin daga ba

Shugaba Trump ya yi wa Koriya ta Arewa barazana da kalamai marasa dadi, irin kalaman da shugabannin Amurka ba su saba furtawa ba, sai dai hakan ba ya nufin Amurka a shirye take ta fara yakin ba.

Wani jami'in sojin Amurka da ya bukaci a boye a sunansa ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa, "saboda kawai suna yin munanan kalamai, ba zai sauya akidinmu ba".

Wani mai sharhi a jaridar New York Times, Max Fisher, ya yi amannar cewa,"Wadannan wasu kalamai ne na wasu mutane, amma ba matsayin shugabanni ba, wanda shi ne jigo a dangantaka tsakanin kasashe.".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption China ce babbar kawar Koriya ta Arewa

Me ya yi saura, bayan gwajin makami mai linzami guda biyu da Koriya Ta Arewa ta yi a watan Yuli, Amurka ta dawo da dabarar yadda za ta takura Koriya ta Arewa ta hanyar takunkumin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta saka mata.

Kuma har yanzu ana ci gaba da tattaunawar diflomasiyya mai ciki da kwarin gwiwa a kan yiwuwar samun sulhu, inda suke samun goyon baya daga China da kuma Rasha.

Wannan yana kalamai masu yin tafka da warwara, amma kuma a bangare guda suna sa Shugaba Trump yana shiga taitayinsa.

Duk da haka wasu masu sharhi na cewa, rashin samun fahimtar juna kan iya jawo yakin da ba a shirya masa ba.

3. Akwai lokacin da Amurka ta kusa gwabza yaki da Koriya ta Arewa

Tsohon Mataimakin Sakataren Harkokin wajen Amurka PJ Crowley ya yi bayanin cewa, Amurka da Koriya ta Arewa sun fara takaddama tun shekarar 1994, a lokacin da Koriya ta Arewa ta ki amincewa ta bar wasu maasu bincike na kasa da kasa su bincike shirinta na kera makami mai linzami.

Daga nan ne harkokin diflomasiyya ya lalace.

A tsawon shekaru, Koriya ta Arewa ta sha yin barazana ga Amurka, da Japan da kuma Koriya ta Kudu, ta kuma sha yi wa makwabciyarta barazana a lokuta daban-daban.

Kalaman Trump na cike da abubuwa, wadanda ba a taba jinsu ba daga wurin wani shugaban Amurka ba.

Mista Crowley ya ce "Amurka ta sha fadar cewa idan Koriya ta Arewa ta kuskura ta kai mata hari, za ta kawo karshen gwamnatin kasar."

Ya kara da cewa dan bambancin a nan shi ne, shugaban Amurka ya ce zai iya fara kai wa Koriyar hari, (kodayake daga bisani Sakataren Harkokin Wajen kasar Rex Tillerson ya kawar da yiwuwar hakan).

Masu sharhi sun ce, irin wadannan abubuwa marasa dadi da ke fitowa daga fadar White House ba a saba ganinsu ba, wanda hakan ya sa ake damuwa.

Har yanzu Koriya ta Kudu wadda babbar kawar Amurka ce, ita ce za ta fi fuskantar matsala daga Koriya ta Arewa - wadda ita ko damuwa ba ta yi.

4. Wanne tasiri yakin Amurka da Koriya zai yi ga nahiyar Afirka?

Dokta Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya ce yakin ba zai yi wani tasiri ga kasashen Afirka ba kai-tsaye saboda babu wata kasa a nahiyar da take hulda da Koriya ta Arewa.

Ya ci gaba da cewa: "A baya Amurka ta yi yake-yake da dama da wasu kasashe amma hakan bai yi wani tasiri ga nahiyar ba."

Sai dai ya ce akwai fargabar cewa "Koriya ta Arewa za ta iya kai wa sansanonin sojojin Amurka da ke nahiyar Afirka," in ji shi.

Har ila yau, ya ce yakin zai iya shafar kasar China - wadda take hulda sosai da kasashen nahiyar "amma ba na ganin China za ta yi fito na fito da Amurka."

Kyari ya ce babban abin tsoro game da yakin shi ne yadda dukansu suke da makamin kare dangi.

"Wannan babban al'amari ne saboda idan aka yi maganar Nukiliya, ana maganar makami ne da zai hallaka miliyoyin jama'a. To ka ga wannan wani abu ne da zai iya jawo Yakin Duniya na Uku, ko kuma tada duniyar ma baki daya," a cewarsa.

Ya ce: "Yakin Amurka da Koriya ta Arewa ba karamin bala'i ba ne don mutum ma ba zai iya hasashen abin da zai faru ba."