Kun san garin da ake korar mata idan suna jinin al'ada?

Thirteen year old Nepalese villager Sarswati Biswokarma sits inside a 'chhaupadi house' in the village of Achham, some 800km west of Kathmandu, on 23 November 2011 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wasu yankunan Nepal mata na komawa can bayan gari idan suna jinin al'ada har sai sun gama

Majalisar Dokoki a kasar Nepal ta gabatar da wata doka da ta hana tilasta wa fitar da matan da suke jinin al'ada daga gidajensu.

A karkashin dokar, duk wanda aka kama da aikata wannan al'adar zai fuskanci daurin wata uku da kuma tarar dala 30.

An haramta yin wannan al'adar ne bayan da wasu mata biyu suka mutu a lokacin da suke bacci cikin wurin da aka killacesu.

Masu fafutuka sun ce dole ne a bi dokar, amma akwai bukatar a kawo sauyi a al'adar.

A tsohuwar al'adar Hindu, ana daukar matan da suke al'ada da wadanda suka haihu a matsayin abin kyama ko wadanda suke jawo asara, inda ake tilasta musu kauracewa gidajensu su koma bayan gari da kwana.

Ana haramta musu taba garken dabbobi da maza, ana hana su yadda za su samu wasu abincin, da shiga bandaki da sauran abubuwan gida, inda ake tilasta musu fita daga gida su tafi can nesa da kauyukansu.

Suna fuskantar tsananin sanyi lokacin hunturu, da kuma samun barazanar mugayen abubuwa, sannan kuma ba sa iya zuwa makaranta.

A watan da ya gabata ma, wata budurwa ta mutu bayan da maciji ya sareta a lokaci da take bacci a wurin da take a killace lokacin da take al'ada da ke nesa da gidansu.

Mutuwarta ta biyo bayan ta wata 'yar shekara 15 a watan Disambar 2016, wacce ta kone sakamakon wutar da ta kunna a wurin da take kwana don ta ji dumi.

A shekarar 2005 ne gwamnatin Nepal ta saka dokar a hukumance, sai dai a lokacin ba a saka tara ba, inda aka ci gaba da yin al'adar a yankunan karkarar yammacin Nepal.

Sabuwar dokar da aka gabatar ranar Laraba ta tabbatar da cewa, za a hana fitar da matan da suke al'ada ko suka haihu daga gidajensu, ko hana su yin wasu abubuwa na gida ko kuma yi musu wani abu da yake nuna wariya ko abun da ya yi kama da haka.

Krishna Bhakta Pokharel, dan majalisa ne kuma shugaban kwamitin zartar da dokar, ya ce, dokar za ta fara aiki a shekara mai zuwa.

"Shekara mai zuwa za mu kaddamar da gangamin wayar wa da mutane kai, da kuma yi musu bayani game da sabuwar dokar," in ji shi.

Wata mai fafatukar yaki da wannan al'adar Pashupati Kunwar, 'yar yammacin gundumar Achham, ta shaida wa BBC cewa, "ta yi matukar farin-ciki da wannan dokar da aka gabatar".

Ta kara da cewa, "Mun dade muna fafatuka wajen wayar da kan mutane a kan wannan al'adar. Yanzu kuma gwamnati za ta saka kaimi wajen tabbatar da dokar."

Apsara Neupane, wanda aka zaba kwanan nan a matsayin mataimakin shugaban gundumar Chandannath da ke yammacin Nepal, ya ce, babbar matsalar ita ce yadda za a sauya dabi'ar mutane."

Ta ce, "Saka doka mai karfi yana da muhimmanci, sai dai sauya al'adun mutane zai dauki lokaci mai tsawo, a ko wanne yanayi ina farin-cikin ganin an samu wannan sauyi, yadda mutane za su daina wannan mummynar al'ada".

A wani rahoto da sashen kare hakkin dan'adam na Amurka ya fitar, an nuna cewa, adadin da aka samu na binciken da aka yi na shekarar 2010 a Nepal, kashi 19 cikin 100 na matan da suke da shekara 15 zuwa 49 ne suke gudanar da wannan al'ada a fadin kasar.

Labarai masu alaka

Karin bayani